Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-nahar cewa, kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty Interntional ta yi kakkausar suka dangane da kisan palastinawa da Isra’ila take yi babu ji ba gani a cikin kwanakin nan.
Kungiyar kare hakin bil-adama ta kasa da kasa ta yi alawadai kan yadda haramcecciyar kasar Isra'ila ke take hakin bil-adama kan Al'ummar Palastinu A wata sanarwa da ta fitar yau.
Wannan kungiyar Amnesty international ta ce ministan harakokin tsaro na cikin gidan Isra'ila Gal'ad Ardan ya kamata ya bayyana damuwarsa kan binciken da za a gudanar na karya hakin bil-adama da Ma'aikatar sa ke yi kan Al'ummar Palastinu.
Sannan ta ce Gwamnatin Isra'ila,na kame Al'ummar Palastinu ba tare da wani laifi ba,ba kuma kan ka'ida ba, tana amfani da Sojoji cikin farin kaya domin muzgunawa Al'ummar Palastinu, sannan kuma tana azabtar da fursinoni gami da tsare kananen yara da shekarunsu bai kai a tsare su ba a gidan kaso ba.
Dukkanin wadannan laifuwa ne dake tabbatar da cewa gwamnatin haramcecciyar kasar Isra'ila na take hakin bil-adama a fili.
3409292