IQNA

Wajibi Ne A Yada Sahihiyar Fahimtar Kur’ani A Tsakanin Matasa Musulmi Domin saita Tunaninsu

18:32 - October 30, 2015
Lambar Labari: 3417486
Bangaren kasa da kasa, malamai da masana da suke halartar taron tabbur na kr’ani mai tsarki a birnin Kazablanka na kasar Morocco sun jaddada wajabcin yada sahihiyar fahimta ta kur’ani a tsakanin matasa musulmi domin saita tunaninsu.


Kamfamnin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Almisriyun cewa, fiye da malamai da masana 500 ne suka halarci taron tadabbur kan kur’ani mai tsarki a Kazablanka na Morocco da ya kawo karshe.

Malamai da masana da suka halartar taron tadabbur na kr’ani mai tsarki a birnin sun jaddada wajabcin yada sahihiyar fahimta ta kur’ani a tsakanin matasa musulmi domin saita tunaninsu bisa sahihiyar koyarwa ta wannan littafi mai tsarki.

Wannan kira ya zo bisa la’akari da halin da matasan musulmi ske ciki ne a halin yanzu na shiga rudu sakamakon yawo da hankalinsu da waus kiye da ke kirean kansu malamai, wadanda ke sanya s shiga ayyukan ta’addanci da sunan addini, wanda hakan yake ci gaba da bakanta sunan wannan addini.

Taron ya kawo karshe wanda ya gudana da taron tare da sanya idon babbar cibiyar da ake kula da traukan tadabbr a cikin kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa, kuma an kammala taron a cikin kwanaki biyu da aka kwashe ana gdanar da shi.

Wasu daga cikin abubuwan da aka mayr da hankalia  akansu akwai bayani kan hakikanin abin da ake kira tunania  cikin ayoyin kur’ani mai tsarki, wanda shi ne zai bayar da dama zuwa ga hakinain tadabbur da ake nufu a cikin wannan littafi mai tsarki.

A kan haka ne wasu daga cikin wadanda suka gabatar da jawabi ko makaloli a wurin sun yi ishara da cewa, tunani shi kadai kan ayoyin kur’ani bas hi tadabbur ba, domin kuwa tadabbur yana zuwa a lokacin da ake tnani domin gano ma’anoni da hikimomin bangiji da suke cikin ayoyin da ake karantawa daga liottafin.

Wannan babbar cibiya dai an gina ta tun a cikin shekara ta 1433 kuma ba ta gushe ba tana ci gaba da gudanar da ayykanta da kuma taruka na watanni da kuma na shekara a cikin kasashen musulmi da na larabawa.

3415457

Abubuwan Da Ya Shafa: morocco
captcha