Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «Long Island Press» cewa, an bude wannan cibiya ta hada kan addinai a kasar Amurka da nufin kara fadada kusanto da juna a tsakanin addinai baki daya.
Faruk Khan wani likita musulmi mazaunin birnin New York ya bayyana cewa, ayyukan wannan cibiya za su taimaka wajen samar da kyakywar fahimta da bayyana mahanga ta kowane addini dangane abin da ya kunsa kuma yake koyarwara.
Ya ce musamman ma a gare su musulmi hakan yana da matukar muhimmanci, domin kuwa ko ba komai hakan zai ba su damar yin bayani kan addininsu da kuma manufoffinsa na zaman lafiya atsakanin dukkanin al’ummomin duniya mai maon yadda ake bayyana ma al’ummomin turai sabanin yadda yake.
Daga cikin ayyukan da wannan cibiya za ta rika aiwatarwa har da shirya gudanar da taruka a cikin gundumar New York da kewaye domin tunatar da mabiya addinai wajabcin zaman lafiya da juna.
An kafa wannan cibiya ta Long Island tun kimanin shekaru ashirin da suka gabata, amma adai a cikin shekarun baya-bayan nan cibiyar ta kara bunkasa ayyyukanta.
Sakamakon bincike da kuma jin ra’ayin jama’a ya nuna cewa a cikin shekara ta 2010 ya zuwa addinin mulsunci shi ne addinin da yafi saurin karbuwa a kasar ta Amurka.
Yanzu haka dai akwai kimanin musulmi miliyan 8 a kasar ta Amurka baki daya.
3421630