Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bawwaba veto cewa, Oprah Winfrey a cikin sabon shirin nata mai suna belief za ta bayyana matsayin kauna da soyayya a cikin addinin muslunci.
Matar da tafi dukkanin matan suniya kudi za ta fara gabatar da wannan shirinne a matsayin sabon shirin talabijin da za ta rika gudanarwa kan addinai.
Oprah Winfrey: Zan Nuna Wasu Hotuna Na Makka Ga ‘Yan Kallo
Ta ce a cikin wanann sabon shirin nata za ta nuna wasu himman wurare na muslunci daga birnin Makka masu tsarkia wajen musulmi.
Oprah Winfrey ta kara da cewa za ta iyakcin kokarinta acikin wannan shiri domin bayyana al’adun mulsunci.
Wannanya faru sakamakon wani mataki da wasu suka dauka a daya daga cikin manyan jami’oin Amurka wato jami’ar California, inda suke nuna damuwa kan addinin muslunci, wanda hakan ya sanya suke tsananin kiyayya da shi saboda tsoron da suke ji dangane da shi.
Hakan ya sanya wani mai gabatar da shirin talabijn daukar nauyin fara gudanar da wani shiri na kiyayya da muslunci domin bata sunan wannan addini.
Oprah Winfrey ta ce a cikin sabon shirin nata za ta yi kokarin ganin ta kawar da tsoron da Amurkawa suke da shi dangane da addinin muslunci, tare da tabbatar musu da cewa shi addini na zamantakewa, ban a tashin hankali ba kamar yadda ake nuna musu.
3421594