IQNA

Masu Tafiya Zuwa Taron Arba’in sun Fara Tattaki Zuwa Karbala

16:28 - November 12, 2015
Lambar Labari: 3447487
Bangaren kasa da kasa, masu aniyat tafiya taron Arba’in na Imam Hussain sun fara kama hanya zuwa birnin karbala domin halartar wadannan taruka.


Kamfanin dilalncin labaran kur’ani na Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na kamfanin dilalncin labaran Rasa cewa, dubban daruruwan mutane a daga sassa na Iraki sun fara kama hanyar zuwa taron arbain.

Hojjatol Islam Sayyid Izzuddin Hakim wakilin Ayatollah Sayyid Muhammad Saed Hakim ya bayyana cewa, wannan babban lamari ne dangane da matsayin limaman gidan shiriya masu tsarki, domin kuwa mutane suna tafiya ne bisa imaninsu na yarda da manzo da iyalan gidansa da kuma girmama su.

Miliyoyin mutane suna ci gaba da tafiya zuwa birnin karbala na kasar Iraki domin halartar tarukan Arba'in na shahadar Imam Hussain (AS) da za a gudanar hubbarensa da ke birnin.  

Mai aiko ma tashar talabijin ta al-alam rahotani daga kasar Iraki ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu dai miliyoin mutane suke tafiya a kasa daga sassa daba-daban na kasar Iraki a kan hanyarsu ta isa birnin na Karbala.

Kamar yadda baki daga kasashen ketare suke isa kasar ta Iraki a iyakokinta na kasa da kuma filayen safkar jiragen sama a biranan kasar.

A nata bangaren rundunar 'yan sanda a kasar ta sanar da kammala daukar dukkanin matakan da suka dace domin bayar da kariya ga masu tarukan na addini, inda yanzu haka jami'an tsaro na hadin gwiwa tsakanin sojoj da 'yan sanda fiye da talatin suke ciki da wajen birnin na Karbala suna gudanar da ayyukansu na tsaro.

3447402

Abubuwan Da Ya Shafa: karbala
captcha