Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-alam cewa, rundunar tsaro ta kasar Iraki ta bayar da tabbacin faruwar tagwayen hari biyu a kan wata Hussainiya da ke kusa da Baghda wanda ya yi sanadiyyar yin shahada da kuma jikkatar mutane da dama.
Wani Jami’in soji Sa’ad Ma’in ya bayyana a wqata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Saumariyya News cewa, an kai harin a kan Husainiyar Baqiyyatollah da ke cikin garin na Sadr a kan mutane da suke wurin.
Wannan dai bas hi karon farko ko a kwanaki 5 da suka gaba mutane 7 ne suka rasa rayukansu a wurin sakamakon hari.