IQNA

Hare-Haren Ta’addanci A wata Hussainiya A Garin Sadr Da Ke Baghdad

22:32 - November 13, 2015
Lambar Labari: 3447716
Bangaren kasa da kasa, an kai wasu tagwayen hari biyu a kan wata Hussainiya da ke kusa da Baghda wanda ya yi sanadiyyar yin shahada da kuma jikkatar jama’a.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-alam cewa, rundunar tsaro ta kasar Iraki ta bayar da tabbacin faruwar tagwayen hari biyu a kan wata Hussainiya da ke kusa da Baghda wanda ya yi sanadiyyar yin shahada da kuma jikkatar mutane da dama.



Wani Jami’in soji Sa’ad Ma’in ya bayyana a wqata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Saumariyya News cewa, an kai harin a kan Husainiyar Baqiyyatollah da ke cikin garin na Sadr a kan mutane da suke wurin.



Wannan dai bas hi karon farko ko a kwanaki 5 da suka gaba mutane 7 ne suka rasa rayukansu a wurin sakamakon hari.



3447652

Abubuwan Da Ya Shafa: iraki
captcha