Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «OKCFox» cewa, mabiya addinin muslunci na birnin Oklahoma na jahar Oklahoma ta kasar Amurka ne suka shirya gudanar da wannan taro.
Adam Sultani daya daga cikin masu shiya taron ya bayyana cewa, za su gudanar da wannan taro ne da nufin kara kusanto da fahimta a tsakanin mabiya addinai na jahar, da kuma kara fahimtar da su koyawarwar muslunci.
Ya ci gaba da cewa abubuwan da suka faru a biranan Paris da kuma Beirut sun kara tabbatar da cewa wadanda suke ke kai irin wadannan hare-hare ba su da wala alaka da addinin muslunci, illa dai kawai su suna kiran kansu musulmi, amma abin da suke bas hi da watala da muslunci.
Haka nan kuma ya ce suna kokarin ganin sun karafa sulhu da ke tsakaninsu da sauran mabiya addinai na daban, domin hakan yana da matkar muhimmanci wajen kara fito da matsayin muslunci na son zaman lafiya.
Kungiyar ta’addanci ta Daesh ta sanar da cewa ita ce take da alhakin kai hare-haren Beirut na Lebanon da kuma Paris na kasar Faransa.
3451700