IQNA

Za a Rufe Masallatan Masu Tsattauran Ra’ayi A Cikin Kasar Faransa

16:45 - November 16, 2015
Lambar Labari: 3453384
Bangaren kasa da kasa, ministan harkokin cikin gida na kasar Faransa ya bayyana cewa za su dauki matakin rufe duk wasu masallatai da ake yada tsatsauran ra’ayi a kasar.


Kamfanin dilalcnin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na (Bernard Cazeneuve) cewa  ministan harkokin cikin gida na kasar Bernard Cazaeneuve ya sanar da cewa gwamnatin Faransa na nazarin hanyoyin rushe tsarin masalatai kasar masu kaifin ra’ayin addini islama.

Wannan dai na zuwa kwana biyu bayan mumanen hare-hare da sukayi sanadin mutuwar mutane sama da darida ashirin da tara tare da raunana wasu dari uku da hamsin a ranar juma’a data gabata.

A cikin matakin na ba sani ba sabo da za’a tattauna a taron ministoci, hukumomin kasar sun ce babu sassauci ga masu yadda akidar kaifin kishin addini a cikin kasar.

Wannan mataki dai ya zo sakamakon abin da ya faru a kasar ta faransa a cikin makon da ya gabata na kai hare-hare a cikin babban birnin kasar wanda hakan yay i sanadiyyar mutuwar mutuwar mutane da dama, tare da jikkatr wasu  da dama.

3453223

Abubuwan Da Ya Shafa: faransa
captcha