IQNA

Kungiyar Musulmin Faransa Ta Yi Kira Da A Yi Allawadai Da Ta’addanci A Sallar Juma’a

19:15 - November 19, 2015
Lambar Labari: 3454600
Bangaren kasa da kasa, babbar kungiyar musulmi a kasar Faranasa ta kirayi limaman juma’a na kasar da su yi Allawadai da duk wani aikin ta’addanci da kuma masu aikata shi a gobe Juma’a.


Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya nakalto daga jaridar Almisriyun da ake bugawa  akasar Masar cewa, Muhamamd Albushari shugaban babbar kungiyar musulmin kasar Faransa, ya ce suna kira ga dukkanin musulmi a cikin kasar farasa da am duniya bakidaya, da su yi Allawadai da harin ta’addanci.

Bushari ya ce musulmin da suke zaune a nahiyar turai su ne suka zama ragon layya na ayyukan ta’addancin da ake yi da sunan Musulunci, ya ce ‘yan ta’addan suna bata sunan muslunci.

Musulmin kasar Faransa sun kirayi limamansu da su fito fili su soki lamirin duk wani dan ta’adda, kuma su nisanta addinin muslunci da wadannan mutane da mumman aikin da suke yi da sunan wannan addini mai tsarki.

3454490

Abubuwan Da Ya Shafa: faransa
captcha