IQNA

Moqtada Sadr Ya Kare ‘Yan shi’a Na Kasar Algeriya

19:16 - November 19, 2015
Lambar Labari: 3454601
Bangaren kasa da kasa, Moqtada Sadr ya kare mabiya tafarkin shi’a a na kasar Algeriya inda ya ce hakan yana a matsayin kare wadanda a ke zalunta ne.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Iram News cewa, Moqtada sadr shugaban mabiyar Sadr a Iraki a cikin jwabinsa karo na biyu a kan ‘yan shi’a na Algeriya yak are su, tare da mayar da martanni a kan ministan kula da harkokin addini na kasar.

Ya ce: shi ba yana kare ‘yan shi’a ne ba domin saboda wani lamari, ko kuma neman samun wani matsayi na siyasa, yana yin hakan ne domin neman hakkokinsu na ‘yan kasa ta fuskar zamantakewa, akida, addini da kuma siyasa.

Hakan kuma ya kara da cewa baya neman yabon wani daga cikinsu, yana yin hakan ne domin kawai yak are hakkokins a  matsayin wadanda ake zalunta.

Moqtada Sadr kafin wannan lokain dai ya yi kira ga mabya tafarkin shi’a a kasar Algeriya da cewa kada su zama kifin rijiya, ya kamata su rika gudanar da lamurransu na addini, lmarin da ya sanya ministan kula da harkokin addinin kasar mayar da martani da cewa masallatai ba wurin tarukan shi’a ba ne.

3454485

Abubuwan Da Ya Shafa: iraki
captcha