Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na NUN cewa, babbar cibiyar kula da ayyukan hubbaren Imam Hussain (AS) ta ce ta samar da kamarori dari takwas da aka kafa a wurare a cikin birnin Karba da kewaye domin sanya ido kan tarukan Arbain na wannan shekara, wanda ya hada har da kan titunan birnin.
Rasul Abbas Fadal mai kula da harkokin tsare-tsare ta fuskar sanya ido kan ayyukan nauori a hbubbaren Imam Hussain (AS) y ace sun dauki wannan mataki ne domin tabbatar da tsari da kuma tsaro.
Ya ce kasantuwar wannan taro yana samu halartar miliyoyin mutane daga koina, shi yasa suka dauki matakin kara yawan kamarori da suka kai 800 wadanda suke kallo tare da daukar duk wani motsi na mutane baki daya.
Ya kara da cewa injiniyoyi da suke aiki a karkashin wannan cibiya ne suka kafa kamarorin kuma suka hada su da wurin da ake kallon kowane da aikinsa.
A bangare gda kuma ya ce baya ga kafa kamarori 800 a wurare daban-daban, akwai wasu kamarorin na musamman guda 1000 da aka kafa wadanda suke kula daidaikun mtane domin tantance su da kuma irin abubuwan da suke dauke da su.
Daga karshe ya rufe da cewa yanzu haka dai sun kammala dukkanin shirinsu ta wannan fuska, kuma suna fatan a gudanar da wadanann taruka masu albarka cikin koshin lafiya kuma a gama lafiya.
3457152