A zantawarsa da kamfanin dilalncin labaran Iqna Ali Akbar Diyai ya ce, sakon na jagora yana taatre da muhimamn lamurra da suka ja hankalin matasan turan wajen jawo fahimtarsu kan matasayar addinin muslunci danagne da ta’addanci.
Sakon ya kuma kara da cewa hari na karshe karshen nan da yan ta’addan suka kai birnin Paris na kasar faransa, wanda ya hargitsa harkokin zamantakewa a kasar da kuma wasu kasashen turai, ya zama darasi ga wadanda suke jin irin abubuwan da suke faruwa a kasashen Musulmi wadanda suka dade cikin wannan halin. Abin bakin ciki inji jagoran.
Shi ne wasu kasashen yamma suna goyon bayan wadan nan yan ta’addan har ma suna masu rarrabasu tsakanin masu kyau da marasa kyau.
Jagoran ya rubuta wannan sakon ne ga matasa a kasashen yamma, don sanin cewa matasan sune wadannan yan ta’adda suke farauta don shiga cikinsu, ganin cewa gogewarsu a harkar rayuwa kadan ne, kuma su ne suke da zukata masu tsarkin da zasu iya karban gaskiya a duk lokacinda ta zo masu.
Wannan dai shi ne sakon jagoran na biyu bayan wanda ya rubutawa matasan a cikin watan Jenerun shekara ta dubu biyu da hudu bayan harin da wasu yan ta’addan suka kan ofishin wata mujalla a birnin Paris na kasar Faransa. Sakonnin guda biyu dai suna kira ne ga matasan kasashen yamma musamman kasashen Turai da Amurka na su fahinci wannan gaskiyar kafin su fada cikin tarkon yan ta’adda masu wuce gona da iri da sunan addinin da basu sanshi ba.
Har’ila yau sakonnin biyu dai sun yi ishara ga yadda shuwagabanni da kuma yan siyasa a kasashen yamma da Amurka suke goyon bayan yan ta’adda wadanda suke kira “masu matsakaicin ra’ayi.
Don suna zaton wadan nan yan ta’addan zasu zama masu amfani a garesu, don zasu kasu ga cimma manufifinsu a kasashen musulmi. Amma wadanda suke cutar da su kuma sune yan ta’addan ta yakamata a yake su.
Jagoran ya bayyana cewa matukar yan siyasar kasashen yamma sun ci gaba da daukar yan ta’adda kamar yadda suke a halin yanzu, to kuwa babu ranar da za’a kawo karshen ta’addanci a duniya.
Sakonnin zuwa matasa kasashen yamma sun jaddada bukata ga shuwagabannin kasashen yamma na su daina dorawa sauran kasashen duniya al’adunsu wadanda suka bambanda ta na sauran mutanen wadan nan kasa she.
3460253