IQNA

Masu tsatsauran Ra’ayi Suna Kallon Zahirin Ayoyin Kur’ani Ne

23:41 - December 11, 2015
Lambar Labari: 3462161
Bangaren kasa da kasa, Ahmad Ibadi shugaban majalisar malaman Muhammadiyyah a kasar Morocco ya bayyana cewa masu tsatsauran ra’ayi suna kallon zahirin ayoyin kur’ani ne kawai.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «alyaoum24.com» cewa, Ahmad Ibadi shugaban majalisar malaman Muhammadiyyah a kasar Morocco a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a gaban wani taro na mamamaln Afirka a jiya, ya bayyana cewa masu tsatsauran ra’ayi suna kallon zahirin ayoyin kur’ani ne kawai ba tare da sanin hakikanin fassara ta badininsu ba.



Ya ci gaba da cewa dukkanin ayoyin da suke kallo suna aikata ta’addanci bisa fakewa da su ayoyi kimanin 500 ne da ke cikin kur’ani, alhali kuwa  akwai ayoyi a cikin kur’ani da suka kai 6236 a cikin wannan littafi mai tsarki, wadanda suka kawai da kai daga gare su da koyarwarsu.



Dangane da yadda ya kamata a fuskanci wannan lamari kuwa, mamalmin ya ce, nauyi ne da ya rataya kan masana da malamai da su mike domin su ilmantar wa da wadannan mutane tare da rusa shubhohin da suke kawo da ayoyin kur’ani mai tsarki wadanda sub a su fahimce ba.



Ya ce idan malamai suka tashi to za a samu nasarar shawo kan lamarin musamman ma a cikin kasashen nahiyar Afirka, inda mutane suke karbar komai indai ya shafi addini da zuciya bude, idan kuma aka yi sakaci to kuwa wannan lamari zai bazu kuma zai yi illa mai muni.



3462074

Abubuwan Da Ya Shafa: morocco
captcha