Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Kullu Irak cewa, kimanin jami’an tsaro dubu ashirin da biyar ne suke gudanar da ayyykan tabbatar da tsaroa yau Juma’a a lokacin gudanar da tarukan zagayowar ranar rasuwar ma’aiki (SAW) a hubbaren Imam Ali (AS) da ke birnin Najaf.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro yana daya daga cikin taruka na tarihi da aka saba gudanarwa a kasar Iraki baki daya, kamar yadda kuma hubbaren Imam Ali (AS) da ke Najaf ya zama babban wuri da ake gudanar da taruka na bai daya domin tunawa da wannan rana.
Kamfanin dilalncin labaran Saumaria News ya bayar da rahoton cewa, magajin garin birnin na Najaf Lui Alyasiri ya bayyana cewa, jami’an tsaro dubu 25 ne suke gudanar da ayyuka a wannan rana, domin bayar da kariya ga masu gudanar da tarukan a hubbare mai tsarki.
]Ya kara da cewa akwai dubban mutane kuma da suka sa kansu yin aiki na bayar da tsaro tare da hadin gwiwa da jami’an tsaron kasar, domin tabbatar da cewa an gudanar da tarukan cikin nasara.
Daga karshe y ace ko shakka babu ranar rasuwar manzon Allah (SAW) rana mai girma a wajen muminai, saboda hakan ne ne ake samun halartar mutane daga kojna cikin iraki da sauran kasashen duniya zuwa wannan hubbaren Imam Ali (AS) domin halartar tarukan wannan rana.