Kamfanin dilalncin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Mir’at Bahrain cewa, wani gawurtaccen dan ta’adda mai suna Abu Jarrah Alansari ya kirayi mabiyansu a kasashen Saudiyya da Bahrain da su kai hari kan mabiya tafarkin shi’a.
Abu Jarrah Alansari shi ne bababn mai magana da yawun kungiyar ta yan ta’ddan Daesh a cikin kasashen, kuma ya tsani yan shi’a dama tun kafin wannan lokaci.
Kasar da mabiya tafarkin shi’a suka fi yawa a cikin kasashen yanin tekun fasha ita ce kasar ta Bahrain inda yawansu yah aura kashi tamanin da bakwai cikin dari.
Abu Jarrah wanda yake daya daga cikin mutanen da ba a san da zamansu ba yana a sahun gaba wajen yin barana ga utanen da su ne suka fi yawa a kasarsu, kamar yadda kuma yake yin barazana ta kash emutanen da sun fi kashi ashirin da biyar cikin dari a kasarsu.
Kungiyoyin ‘yan ta’adda a kasasashen yankin gabas ta tsakiya da mafi yawan kasashen duniya dai suna dauke ne da akida guda ita ce akidar wahabiyanci da kafirta musulmi, kamar yadda kuma a kasashen duniya da wanann akidar ake gane su, sai dai hanyoyin yadda suke fahimtar ta’addanci na da banbanci.