IQNA

UNICEF: Kungiyar Boko Haram Sun Hana Wa Yara Sama Da Miliyan Biyu Karatun Zamani

22:27 - December 22, 2015
Lambar Labari: 3468423
Bangaren kasa da kasa, asusun Taimakon Kananan Yara Na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya sanar da cewa kungiyar Boko Haram ta haramta wa kananan yara kimanin miliyan biyu karatu na zamani.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin jaridar yaum Sabi cewa, ya bayyana cewar a rahoton da hukumar ta UNICEF ta fitar a yau din nan Talata ta bayyana cewar sakamakon rashin tsaron da kungiyar Boko Haram ta haifar a kasashen Nijeriya, Kamaru, Chadi da Nijar, hakan yayi sanadiyyar hana sama da kananan yara miliyan biyu tafiya makaranta.

Shugaban hukumar UNICEF na Yammacin Afirka Manuel Fontaine ya bayyana damuwarsa ainun dangane da wannan matsalar wanda hakan zai iya kara matsaloli na zamantakewa da yankin yake fuskanta.

A wannan wata na Disamba ma dai kungiyar Boko Haram din sun sanar da cewa za su kara kaimi wajen sace yara 'yan makaranta a kokarin da suke yi na ganin sun hana karatun Boko wadanda suke ganinsa a matsayin haramun a yankin.

3468247

Abubuwan Da Ya Shafa: boko haram
captcha