IQNA

Wasu Musulmi Sun Kare Kiristoci Daga Harin ‘Yan Ta’adda A Kenya

22:10 - December 23, 2015
Lambar Labari: 3468881
Bangaren kasa da kasa, wasu musulmai da ke tafiya a cikin motar haya da mayakan yan ta’adda suka tare a Kenya sun kare fasinjoji Kiristoci da ke tare da su a cikin motar.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Guardian cewa, Mahmud saleh daya daga cikin matafiyan yana cewa, duk da cewa akwai yiyiwa mayakan na alshabab su halakasu gaba daya musulman sun ki ware wa har sai yan ta’addan suke tafi.

 

Musulmai a wani hatsarin da ya auka masu a arewacin Kenya sun taimaki kiritocin da suke tare da don su tsira da ransu. Kamfanin dillancin labaran Farsnews na kasar Iran ya nakalto wani musulmi wamda yake cikin mutanen da mayakan kungiyar alshaban goma  sufa tsaida motar bus da suke cikinta a wani wuri a arewacin kasar ta Kenya.

Inda yace suka bukaci musulmi su ware daga kiritoci ammam suka ki yin haka, sannan wasunsu ma suka bawa kiristocin da suke tafiya tare wasu kayakinsu kamar dan kwali da dogayen riguna don su boye Kaman ninsu.

 

Duk da cewa akwai yiyiwa mayakan na alshabab su halakasu gaba daya musulman sun ki ware wa har sai yan ta’addan suke tafi.
A cikin shekara ta 2011 Kenya ta fusknci a irin wadannan matsaloli na tsaro daga yan ta’addan Shabab na kasar Somalia.

Haka nan kuma  kwanakin baya ma yan ta’addan sun kashe mabiya addinin kirista 28 a cikin motar bus a wani yanki na kasar.

3468520

Abubuwan Da Ya Shafa: kenya
captcha