IQNA

Musulmi Su Yi Riko Da Koyarwar Addini / Amurka Ba Ta Amince Da Musulunci Na Asali Ba

8:54 - January 03, 2016
Lambar Labari: 3480009
Bangaren siyas, Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamenei jagoran juyin juya halin muslunci ya bayyana jiya a lokacin da yake ganawa da baki mahalarta taron makon hadin kai gami da jakadun kasashen msuulmi da kuma jami’an kasar cewa; ya rataya kan al’ummar musulmi ta ta zama cikin fadaka da lura da kuma yin rikon da koyarwarwannan addini ta hakika.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin yanar gizo na ofishin jagora tarjamar matanin bayanin nasa da ke cewa, a jawabin da ya gabatar yayin wannan ganawar, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya taya al'ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah (s.a.w.a) da Imam Sadiq (a.s) inda ya bayyana kokari ba kama hannun yaro wajen sake rayar da ruhi na hakika na addinin Muuslunci a wannan duniya wacce take cike da zalunci da nuna wariya da rashin imani a matsayin daya daga cikin mafi muhimmancin nauyin da ke wuyan duniyar musulmi a halin yanzu musamman a tsakanin malamai da masana. Jagoran ya ci gaba da cewa: A halin yanzu dai lokaci ne da duniyar musulmi da za ta mike wajen tabbatar da ci gaba iri na Musulunci ta hanyar amfani da ilimi, hanyoyi na zamani da kuma hankali, hikima da basira.
Ayatullah Khamenei ya bayyana gudanar da bukukuwan maulidin Annabi (s.a.w.a) kawai a matsayin wani karamin aiki idan aka kwatanta irin gagarumin nauyi da fatan da ake da shi a kan duniyar musulmi inda ya ce: A halin yanzu nauyin da ke wuyan al'ummar musulmi bai takaita kawai ga gudanar da bukukuwan maulidi ko ranar aiko Ma'aiki (s.a.w.a) ba, face dai wajibi ne duniyar musulmi ta ba da himma da muhimmanci wajen isa ga hakikanin ci gaba da kuma koyarwa ta Musulunci.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Sabuwar wayewa ta Musulunci ba tana nufin wuce gona da iri kan kasashe, take hakkokin bil'adama da kuma tilasta wa al'ummomin halaye da al'adunsu tamkar irin abin da al'adu da ci gaban yammaci ya aikata. Face dai abin nufi shi ne gabatar da kamala da nagarta ta Ubangiji ga bil'adama da kuma share fagen da mutum zai gano wa kansa ingantacciyar hanya da kuma tafarki.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin yadda kasashen yammaci suka yi amfani da ilimi da falsafar duniyar musulmi wajen kafa irin ci gabansu, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewar: Irin wannan ci gaban, duk kuwa da a zahiri ya gabatar da abubuwa masu kyau da suka hada da fasaha, sauki da kayayyakin aiki na saukake rayuwa, to amma dai bai samar wa dan'adam da farin ciki da sa'ada da kuma adalci ba. Sannan ana samun karo da junan a cikinsa.
Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Ci gaban yammaci duk da irin kyawu na zahiri da yake da shi, amma a halin yanzu a bangaren kyawawan halaye da ababe masu kusata mutum da Allah ya zamanto holoko, ta yadda hatta su kansu mutanen yammaci suna fadin hakan.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da cewa a halin yanzu dai lokaci ne na duniyar musulmi su gabatar da kuma kafa tushen koyawa da al'adun Musulunci da gabatar da shi ga duniya, Jagoran cewa yayi: Don isa ga wannan manufar, lalle babu wani fata da ake da shi a kan ‘yan siyasar duniyar musulmi. Don haka wajibi ne malami da masanan da ba su dauki kasashen yammaci a matsayin alkiblarsu ba, su mike wajen wayar da kan musulmi da kuma fahimtar cewa lalle ana iya kafa tushen wannan ci gaban.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin dama da karfin da duniyar musulmi take da shi da suka hada da kasa mai kyau, bigire mai kyau wanda kuma ya dace, albarkatun kasa ba iyaka da kuma al'ummar da suke cikin shiri, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: Matukar aka hada irin wannan karfi da dama da ake da su da hakikanin koyarwar Musulunci, to kuwa al'ummar musulmi za ta iya bayyanar da irin wannan kwarewa da take da shi a fagagen ilimi da siyasa da fasaha da kuma zamantakewa.
Ayatullah Khamenei ya bayyana tsarin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayin misalin da ke tabbatar da yiyuwar isa ga wannan manufa mai girma, daga nan sai ya ce: Iran, kafin nasarar juyin juya halin Musulunci, ta ci baya ainun a fagen ilimi, siyasa da zamantakewa. A fagen siyasa ta kasance saniyar ware, a fagen gudanar da kasa kuwa ta kasance ‘yar amshin shata. Amma a halin yanzu albarkacin Musulunci, al'ummar Iran ta bayyanar da irin matsayi da mutumcin. Ta zamanto kasa ma'abociyar ci gaba mai muhimmanci a fagen ilimi da fasaha da ilmummuka na zamani. Ta zamanto daga cikin kasashen da suke a sahun gaba-gaba a wadannan fagage.
Jagoran ya bayyana cewa ana iya tabbatar da wannan misali a dukkanin kasashen musulmi. Jagoran ya ce: Akwai sharadin isa ga wannan matsayin, sharadin kuwa shi ne raje irin ikon da ‘yan mulkin mallaka na duniya suke da shi a kan al'ummomi, duk kuwa da cewa akwai wahalhalun da za a fuskanta. Don kuwa ba za a iya cimma wata babbar manufa ba tare da wahala ba.
Yayin da yake jaddada cewar a mahanga da ci gaban Musulunci, sabanin ci gaban yammaci, ba a tilasta wa wata kasa da karfin tuwo ta shigo ciki, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Yayin kafa sabuwar ci gaban musulmi, bai kamata mahangarmu ta koma ga kasashen Yammaci ba. Bai kamata mu damu da fara'a da sakin fuskarsu ba. Face dai wajibi ne mu ci gaba da tafiya a bisa ingantaccen tafarki ta hanyar dogaro da irin karfin da muke da shi.
Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar daya daga cikin hanyoyin da makiya suke bi wajen ganin sun hana kafuwar wannan ci gaba na Musulunci shi ne haifar da rarrabuwan kai tsakanin al'ummar musulmi, daga nan sai ya ce: Daga lokacin da jami'an Amurka suka fara maganar kan Shi'a da Sunna, tun daga lokacin masana da masu fahimta suka fara nuna damuwa, don kuwa a fili yake cewa suna shirin kulla wani sabon makircin ne wanda ya fi wadanda suka kulla a baya hatsari.
Haka nan yayin da yake jaddada cewa Amurkawa suna adawa ne da asalin Musulunci, da kuma cewa bai kamata a fada tarkonsu kan maganganun da suke yi na nuna goyon bayan wani bangare ba, Jagoran cewa yayi: Maganganun da tsohon shugaban kasar Amurka yayi bayan harin 11 ga watan Satumba na batun yakin salibu (crusade), a hakikanin gaskiya hakan wata alama ce ta yakin ma'abota girman kai da Musulunci.
Har ila yau kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana maganganun jami'an Amurka na yanzu kan goyon bayan Musulunci a matsayin wani abu da ya saba wa hakikanin abin da ke gudana a kas sannan kuma wata alama ce ta munafuncinsu. Jagoran ya ci gaba da cewa: Jami'an Amurka na yanzu ma suna adawa da asalin Musulunci. Sannan kuma sabanin abubuwan da suke fadi, suna kokarin haifar da rarrabuwan kai ne tsakanin musulmi. Misalin hakan kuwa shi ne samar da kungiyoyin ta'addanci irin su Da'esh da sauran kungiyoyi na daban da aka samar da su daga kudaden ‘yan amshin shatan Amurkan da goyon bayansu nasiaysa, sannan kuma suna ta aikata danyen aikin dake faruwa a duniyar musulmi.
Ayatullah Khamenei ya bayyana maganganun da jami'an Amurka suke yi na nuna goyon bayansu ga ‘yan Sunna da kuma adawa da ‘yan Shi'a a matsayin karya tsagoronta inda ya ce: Shin al'ummar Gaza wadanda suke fuskantar irin wannan bakin zalunci da kisan kiyashin ba ‘yan Sunna ba ne ko kuma mutanen Yammacin Kogin Jordan da su ma suke fuskantar irin wannan mafi munin matsin lambar, ba ‘yan Sunna ba ne?
Har ila yau kuma yayin da yake ishara da maganar wani jami'in Amurka na cewa ‘Riko da Musulunci shi ne makiyin Amurka', Jagoran ya ce: A wajen Amurkawa babu wani bambanci tsakanin Shi'a da Sunna. Suna adawa ne da duk wani mutumin da yake son rayuwa karkashin hukunce-hukunce da kuma dokoki na Musulunci sannan kuma yake kokari wajen cimma hakan.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar babbar matsalar Amurkawa da musulmi ita ce riko da koyarwa da kuma hukunce-hukuncen Musulunci da kuma kokari wajen kafa tushen ci gaban Musulunci. Daga nan sai ya ce: Bisa wannan dalilin ne ya sanya daga lokacin da farkawar Musulunci da aka samu ta kunno kai, suka shiga cikin damuwa da kuma kokari wajen ganin sun kawar da ita, wanda sun sami nasarar hakan a wasu kasashen. To amma dai farkawar Musulunci ba abu ne da za a kawar dashi ba. Kuma cikin yardar Allah za ta kai ga manufarta.
Ayatullah Khamenei ya bayyana cewa babbar manufar ma'abota girman kai ita ce haifar da yakin basasa tsakanin musulmi da kuma ruguza tushen kasashen musulmi irin su Siriya, Yemen da Libiya. Jagoran ya ci gaba da cewa: Bai kamata a zuba ido dangane da wannan makircin ba, face dai wajibi ne a yi tsayin daka wajen tinkarar wannan makirci ta hanyar amfani da basira da tsayin daka.
Haka nan kuma yayin da yake kakkausar suka ga shirun da duniyar musulmi suka yi dangane da ci gaba da matsin lambar da ake yi wa musulmin kasar Bahrain haka nan da kuma ci gaba da ruwan bama-baman da ake yi ba dare ba rana a kasar Yemen, da kuma yanayin da kasashen Siriya da Iraki suke ciki da kuma abubuwan da suka faru a baya-bayan nan a Nijeriya, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Me ya sa duniyar musulmi ta yi gum da bakinta dangane da irin wannan bala'i mai sosa rai da aka yi wa wannan malami mai son kawo gyara, hadin kan (musulmi) kuma mumini, kana aka kashe kimanin mutane dubu da kuma kashe masa ‘ya'yansa?
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: Manufar makiyan Musulunci tana da hatsarin gaske. Nauyin da ke wuyan kowa shi ne amfani da basira da kuma farkawa. Sannan kuma a irin wannan yanayin nauyin da ke ruwan malaman Musulunci da masana na gari shi ne su yi magana da mutane da kuma ‘yan siyasar da suke da lamiri da kuma bayyanar musu da hakikanin lamarin.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: A yayin da masu tinkaho da karfi na duniya suke kokarin aiwatar da bakar aniyarsu a kan duniyar musulmi da dukkan karfinsu, lalle bai kamata wani ya gafala da rufe ido kan hakikanin abin da ke a kas ba.
Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musuluncin, sai da shugaban kasar Iran Sheikh Hasan Ruhani ya gabatar da jawabinsa, inda yayin da yake taya al'ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Ma'aikin Allah (s.a.w.a) da Imam Sadiq (a.s), shugaba Ruhani ya bayyana Manzon Allah (s.a.w.a) a matsayin babban abin koyi a fagen kyawawan halaye da tsarki. Shugaba Ruhani ya ci gaba da cewa: Annabi Muhammadu (s.a.w.a) ya zo wa duniya da darasin hadin kai da ‘yan'uwantaka.
Haka nan kuma yayin da yake bayanin cewa a halin yanzu aka bukatar riko da koyarwar Annabin Rahama (s.a.w.a) sama da lokutan da suka gabata, shugaban na Iran ya bayyana cewar: Albarkacin hadin kan al'umma da kuma shiryarwar jagoranmu mai girma sun sami damar samun nasara a kan ma'abota tinkaho da karfi na duniya, kuma wannan nasarar za ta ci gaba da wanzuwa.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da zabubbuka guda biyu da suke gaban al'ummar Iran, wato zaben ‘yan majalisar kwararru ta jagoranci da kuma ‘yan majalisar shawarar Musulunci, shugaba Ruhani ya bayyana wadannan zabubbuka guda biyu a matsayin babbar jarabawa ga al'ummar Iran don haka sai ya ce: Wajibi ne kowa ya zamanto yana tunanin nasarar tsarin Musulunci da kuma kasar Iran ne a yayin wannan zaben.
Har ila yau shugaba Ruhani yayi ishara da gagarumar fitowar da al'ummar Iran suka yi a ranar 9 ga watan Dey 1388 (1999 bayan rikicin zaben shugaban kasa da aka gudanar) don nuna goyon bayansu ga tsarin Musulunci na Iran inda ya ce: Ranar 9 ga watan Dey, rana ce da al'ummar Iran suka fito don kare Gidan Annabci, don kare tsarin Musulunci, dokar kasar da kuma tsarin Wilayatul Fakih da kuma Waliyul Fakih din.
Shugaba na Iran ya ci gaba da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sami irin tsaro da kwanciyar hankalin da take ciki ne albarkacin tsare-tsare da kuma hikima da hangen nesan Jagoran juyin juya halin Musulunci. Don haka za mu iya gode wa wannan ni'imar ce ta hanyar kara hadin kai da kuma taimakon duniyar musulmi wajen ‘yantar da kasashen (duniya) daga ta'addanci da kuma tsoma bakin ‘yan kasashen waje.
Haka nan kuma yayin da yake bayanin cewa makiya sun sanya kasashen musulmi fada da junansu, shugaba Ruhani ya bayyana cewar: Matukar manyan kasashen musulmi suka hada kansu suna masu tunanin matsalolin da suke fuskantar musulmi gaba daya, to kuwa cikin sauki za su iya magance matsalolin da suke fuskantarsu.
Har ila yau yayin da yake bayanain cewa wasu kasashen musulmin maimako a ce sun yi kokarin hada kai da kulla mu'amala ta al'adu da tattalin arziki da junansu amma sai suka koma wajen wasu kasashe da suke wajen wannan yankin nan, Shugaban na Iran ya bayyana cewar: Abin bakin ciki ne yadda wata kasa take bakin cikin nasarar da wata al'umma ta samu a fagen siyasa da kuma mika irin karfi na siyasa da duniyar musulmi take da shi zuwa ga manyan kasashen duniya ‘yan waje.
Shugaban na Iran ya ci gaba da cewa: Kasar da ta taka gagarumar rawa wajen faduwar farashin man fetur, amma a yanzu sai ga shi tana fuskantar matsalar tattalin arziki cikin kasafin kudinta na shekara, wanda lamari ne ke nuni da cewa in za ka gina ramin mugunta gina shi gajere.
Daga karshe dai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya gaisa hannu da hannu da wani adadi mai yawa na baki ‘yan kasashen waje da suka halarci taron Makon Hadin Kai.
3470656
captcha