Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Ahmad Hashim Ahmad daya daga cikin mambobin kwamitin gasar kur’ani a Sudan ya sheda cewa, an kawo karshen gasar karatun kur’ani mai tsarki da kuma ilmomin da suka shafe shi ta kasa da kasa kuma za a rufe a laraba mai zuwa idan Allah ya kai mu.
Ya ci gaba da cewa wannan gasa tan adaga cikin wasu muhimman ayyuka da wanna kwamiti nasu yake gudanarwa a kasar ta Sudan, da nufin kara farfado da batun kur’ani da kuma yada koyarwarsa a tsakanin mutanen kasar.
Ahmad Hashim Ahmad ya kara da cewa, daga lokacin da aka fara gudanar da irin wannan gasa, an samu nasarori da dama awannan bangare, kuma hakan sakamko ne na ci gaba da kara bada himma da dukkanin bangarori suke yi.
Daga bangaren yadda ake gudanar da gasar kuwa ya bayyana cewa, ana gudanar da ita nea kowace shekara sau guda, kuma ana gayyatar makaranta daga kasashen musulmi da na larabawa domin su halarta.
A wannan karon an samu halartar makaranta daga kasashe daban-daban, wadanda suka nuna kwazo matuka, kuma za su zama cikin wadanda za su samu kyautukan da za a bayar daga karshe aranar rufe gasar.
An gudanar da gasar ne a bangarori na karatu da kuma harda da hakan ya kama daga juzui na farko zuwa karshe, kamar yadda kuma wasu suka gabatar da harda ko karatu a rabin kur’ani mai tsarki, da ma juzui na 24 kamar dai yadda ya bayyana.
Kimanin kasashe 21 ne suka samu damar halartar gasar tare da wakilansu, kamar yadda kuma kasashe 10 daga cikinsu ban a kasashen musulmi ba ne.
http://iqna.ir/fa/news/3466434