IQNA

15:51 - January 12, 2016
Lambar Labari: 3480043
Bangaren kasa da kasa, kungiyar ‘yan ta’addan daesh ta dauki alhakin kaddamar da harin ta’addanci kan cibiyar kasuwanci a birnin Bagadaza na Iraki.

Kamfanin dillanicn labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar Press TV cewa, harin na jiya yay i sanadiyyar mutuwar mutane 18 tare da jikkatar wasu kimanin 50 na daban.

Maharan dai sun ajiye wata mota da suka shakare da bam a kusa da wurin inda cibiya ce babbata kasuwanci a birnin, kafin daga bisani su tarwatsa ta tare da rike wasu a matsayin garkuwa.

An yi dauki ba dadi a tsakanin mahara da kuma jami’a tsaro bayan kimanin mintuna 90 sun samu nasara kasha biyu daga cikin maharani, da kuma kame wasu hudu, gami yanto wadanda aka yi garkuwa da su.

Wani jami’in ‘yan sanda ya bayyana cewa an shawo kan lamarin, kuma komai yana karkashinsu ba tare da wani haufi ba.

Bisa ga abin jami’an tsaron suka fada 4 daga cikin wadanda aka kasha ‘yan sanda ne.

http://iqna.ir/fa/news/3466755


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: