Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Almanar cewa, babbar cibiyar da ke dakon fatawowin takfiriyya da wadanda suka sha banban a kasar Masar ta gargadi yan kungiyar Ikhwan da cewa su daina yin amfani da sunan jihadi domin kiran mutane zuwa jerin gwanon tuna juyin 25 ga janairu da za su yi.
Bayanin Darul fatwa na kasar Masar ya ce; yan kungiyar ikhwan da wasu bangarori da suke da dangantaka da akidar takfiriyyahm suna ta kiran magoya bayansu da su fito su yi jerin gwano domin tunawa da ranar juyin juya halin kasar, domin yin hakan yana a matsayin jihadi, bayanin ya ce wannan hankoro ne na tunzura jama’a domin tayar da hankali, wanda kuma ya sabawa doka.
Kungiyar Ikhwan dai an sakata a cikin kungiyoyin da aka haramta akasar tare da sakata cikin ‘yan ta’adda tun bayan kifar da Muhammad Morsi, kuma kungiyar ta mayar da ranar 25 ga watan Janairu a matsayin wata rana ta tunawa da juyin juya halin da aka yi a kasar, tare da kiran jama’a da su fito domin tuawa da ita.