IQNA

22:57 - January 26, 2016
Lambar Labari: 3480080
Bangaren kasa da kasa, Jagoran kiristoci mabiya darikar katolika ya bukaci Iran da ta taka rawa wajen warware matsaloli a yanking abas ta tsakiya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na PressTV cewa, jagoran kiristoci mabiya darikar katolika Paparoma Francis a lokacin ganawa da shugaban kasar Iran Hassan Rouhani, ya bukaci Iran da ta taka rawa wajen warware matsaloli na siyasa da fataucin makamai da ta’addanci a yanking abas ta tsakiya baki daya.

Ganawa tsakanin bangarorin biyu ta zo a ziyarar aiki da shugaban kasar Iran yake gudanarwa  akasar Italiya, inda ya gana manyan jami’an gwamnatin kasar, da suka hada da takwaransa na kasar ta Italiya.

A yau ne shugaba Hassan rauhani zai bar kasar ta Italiya, domin kama hanya zuwa kasar Faransa.

3470600

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: