IQNA

Taron Makon Al’adu Daidai Lokacin Issar Rauhani A Faransa

22:34 - January 27, 2016
Lambar Labari: 3480083
Bangaren kasa da kasa, a daidi lokacin isar shugaban kasar Iran a birnin Paris na kasar Faransa za a bude wani taro na makon al’adu na Iran a kasar ta Faransa.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar yada al’adun muslunci cewa, a lokacin da shugaban kasar Iran Hassan Rauhani yake isa a birnin Paris na kasar Faransa za a bude wani taro na makon al’adu na Iran a kasar ta Faransa tare da halartar shugaban, da kuma wasu daga cikin jami’an kasar ta Iran da kuma na Faransa, inda za a baje kolin kayyaykin al’adu da suka hada da abubuwan hannu da sauransu a wurin.

Bayanin ya ci gaba da cewam baya ga shugaba Rauhani,akwai wadanda suke rufa masa daga cikinsu kuwa har da mataimakin babbar cibiyar ta yada al’adun muslunci Mas’ud Sultani far, wanda zai halarci tare da gabatar da bayani kan al’adun kasar ta Iran ga Faransawa da suke da bukatar sanin wani abu kan hakan.

Daga cikin abubuwan da za a baje kolinsu a wurin kuwa, har da kayan kida na zamanin da ya gabata, wanda Iraniyawa suke amfani da s utu daruruwan shekaru, wadanda ake ajiyarsu a matsayin wani abu na al’ada da ba za a manta da shi ba, wanda al’ummar Faransa da dama suke nuna sha’arsu domin sanin wadannan ababe.

Daga karshe za a rufe taron tare da gabatar da jawabai na hadin gwaiwa  atsakanin cibiyoyin yada al’adu na kasashen biyu, wadanda suke da tarihi na tsawon shekaru, duk kwa da matsalolin da aka fuskanta daga bisani sakamakon batutuwa na siyasa tsakanin Iran da kasashen turai.

3470700

captcha