IQNA

22:59 - February 03, 2016
Lambar Labari: 3480106
Bangaren kasa da kasa, a yau ne za a gudanar da wani zaman taro mai taken mahangar Ahlul Bait (AS) a kan kur’ani mai tsarki a cikiyar sayyidah Ruqayyah ta yan kasar saudiyya da ke Qom.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na QAF cewa, cibiyar Ruqayyah ta mabiya mazhabar shi’a na kasar saudiyyah mazauna birnin Qom, sun shirya taro a makarantar Imam Mahdi (AJ) a yau, kan mahangar Ahlul bait (AS) kan kur’ani.

Bayanin ya ci gaba da cewa Sheikh Abdulmuhsen Aljuzairi daya daga cikin manyan malamai na yankin Ihsa na kasar Saudiyya shi ne zai gabatar da jawabi a taron.

Cibiyar sayyidah Ruqayyah (SA) tana bayar da muhimmanci matuka wajen shirya taruka da suka danganci kur’ani mai tsarki ga daliban addini yan kasar ta Saudiyya da suke zaune a birnin Qom, da hakan ya hada da koyar da ilmomin kur’ani da kuma ilimin tajwidi.

Sheikh Abduljalil Almakrani shi ne wandaya shirya tare da daukar nauyin gudanar da wannan taro.

3472574

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: