IQNA

23:00 - February 03, 2016
Lambar Labari: 3480107
Bangaren kasa da kasa, kotun kolin kasar Saudiyya ta yanke hukuncin daurin shekaru uku kan wani dan kasa saboda ya mallaki hoton sheikh Bakir Nimr da kuma tutar kungiyar Hizbullah.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar talabijin ta Alalam cewa, koton kolin ta Saudiyya ta yanke wannan hukunci ne saboda matsayin Hizbullah da kuma yakinta da Isra’ila.

Kamar yadda kotun ta bayyana cewa mallakar hoton sheikh Nimr da kuma tutar kungiyar Hizbullah, alama ce ta shi’a wanda kuma tsarin kasar bai amince da nuna duk wata alama kan hakan ba, inda wasu ke kallon hakan a matsayin wani sabon mataki na nuna bangaranci gay an kasa.

A yan kwanakin da suka gabata ne dai kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amnesty International ta fitar da bayani da ke cewa shekara guda da sarkin Saudiyya ya yi it ace mafi muni a kan hakkokin bil adama  akasar.

Sheikh Nimr Bakir Nimr fitaccen malamain shi’a  akasar ya yi shahada a hannun mahukuntan kasar a karshen watan da ta ya gabata bayan tsare shi na shekaru.

3472507

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: