IQNA

Ministan Al’adun Senegal ya Bukaci;
23:17 - February 14, 2016
Lambar Labari: 3480140
Bangaren kasa da kasa, Imbagnik Indaya ministan kula da harkokin al’adu na Senegala lokacin ganawa da karamin jakadan Iran ya bayyana bukatarsu ta neman Iran ta taimaka wajen shirya fim na Bilal Habashi.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar yada al’adun muslunci cewa, karamin jakadan Iran a Senegal Sayyid Hassan Esmati ya gana da ministan al’adu na kasar ta Senegal.

Karamin jakadan an Iran ya bayyan acewa, kasarsa a shirya take a kowane lokaci ta ci gaba da abin da ta sanya a gaba na kyautata alaka da sauran kasashe, tare da yin aiki tare da su ta fuskoki da dama domin ci gabansu da al’ummominsu da kuma samun sulhu da fahimtar juna.

Ya kara da cewa janye takunkumi kan Iran wata babbar dam ace ta kara fadada wannan buri musamman ma atsakaninta da sauran kasashen msuulmi.

A yayin ganawar tasu ministan kasar Senegal ya bayyana cewa, kasarsa tana isar da sakon taya murna na samun nasar juyin juya hali da ake tunawa da zagayowarsa, sannan kuma ya ce akwai butakar Iran ta taka gagarumar rawa wajen shirya wannan fim.

Ya ce dukkanin al’ummar Senegal suna jiran taimakon Iran wajen ganin cewa aikin wanann fim ya gudana a cikin nasara, musamman ganin cewa na bababn sahabin manzo ne (SAW) kuma mai kiran sala na farko ga manzon Allah.

3475473
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: