IQNA

Jagora A Lokacin Ganawa Da Mutanen Azarbaijan Ta Gabas:

Mutane Su Yi Aiki Sabanin Abin Da Makiya Ke Fata A Lokacin Zabuka

23:39 - February 18, 2016
Lambar Labari: 3480152
Bangaren siyasa, a lokacin da yake ganawa da mutanen Azarbaijan ta gabas, jagoran juyin juya hali ya yi kira da cewa mutane su yi aiki sabanin abin da makiya suke tunani a lokacin gudanar da zabuka masu zuwa.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, a safiyar Laraba ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da dubban mutanen lardin Azarbaijan ta Gabas inda yayin da yake mika godiya da kuma jinjinawarsa ga al'ummar Iran sakamakon fitowar da suka yi kwansu da kwarkwatarsu yayin jerin gwanon ranar 22 ga watan Bahman ya bayyana hakan a matsayin wata alama da ke nuni da tsayayyiyar azama, tsayin daka da kuma farkawar al'ummar Iran, don haka sai ya kiraye su da su yi irin wannan fitowar yayin zaben ranar 7 ga watan Esfand da za a gudanar a kasar don sake jaddada aniyarsu ta kare tsarin Musulunci da ke gudana a kasar bugu da kari kan ‘yanci da kuma daukaka ta kasa. Jagoran ya bayyana cewar: Fitowar mutane cikin basira da sanin ya kamata yayin zaben, zai zamanto bada wa makiya kasa a ido ne.

A yayin wannan ganawar, wadda aka yi ta don tunawa da zagayowar shekarar yunkurin ranar 29 ga watan Bahman shekarar 1356 na mutanen garin Tabriz, Jagoran ya jinjina wa karfafaffen Imani, farkawa da tsayin dakan mutanen lardin Azarbaijan a lokuta masu muhimmanci ga tarihin Iran musamman a lokacin yunkurin juyin juya halin Musulunci inda yayi kira zuwa ga kiyaye matsayin irin wadannan ranaku masu muhimmanci cikin tarihin juyin juya halin Musuluncin, wanda ranar 22 ga watan Bahman daya ne daga cikin irin wadannan ranakun. Jagoran ya ci gaba da cewa: Bisa rahotannin da cibiyoyi abin yarda suka fitar, fitowar da mutane suka yi yayin jerin gwanon ranar 22 ga watan Bahman na wannan shekarar, ta dara na shekarar da ta gabata.

Har ila yau yayin da yake mika godiyarsa dangane da fitowar da mutane suka yi yayin jerin gwanon ranar 22 ga watan Bahman, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Irin wannan karuwar mutanen da suke fitowa wata alama ce da take nuni da cewa ma'abota girman kai sun gaza wajen haifar da gibi cikin azamar da al'ummar Iran suke da ita duk kuwa da kokari ba kama hannun yaro da ma'abota girman kai suka yi wajen ganin an mance ko kuma alal akalla rage kaifin juyin juya halin Musulunci cikin kwakwalan mutane.

Daga nan kuma sai ya koma ga lamarin zaben ‘yan majalisar dokoki da na majalisar kwararru ta jagoranci ta Iran da za a gudanar a ranar 7 ga watan Esfand inda ya ce: Makiya dai suna da wani shiri da makirci da suka shirya don cimma manufofinsu yayin wannan zaben; a saboda haka ya zama wajibi mutane a matsayinsu na masu kasar nan su san wasu abubuwa don hana (makiyan) cimma wadannan manufofi na su.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran ta kawo karshen ikon Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila a Iran, don haka tsawon shekaru 37 din da suka gabata babu wani abin da za su iya da ba su yi ba wajen dakatar da wannan yunkuri na al'ummar Iran. Daga nan sai ya ce: Tun farkon nasarar juyin juya halin Musulunci, makirce-makircen makiya shi ne ganin ba a gudanar da zabe a Iran ba, wanda sun yi iyakacin kokarinsu a wannan bangaren. To amma a lokacin da suka yanke kauna, sai ya zamanto a shekarun baya-bayan nan sun ba da muhimmanci ne wajen sanya alamun tambaya kan zabubbukan da ake gudanarwa, don su sami damar kutsawa cikin zaben da lalata shi.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Sun fara aiwatar da makircinsu dangane da wannan zaben na ranar 7 ga watan Esfand ne da kokarin cutar da matsayin majalisar kiyaye kundin tsarin mulki da sanya alamun tambaya kan matsayar da ta dauka, wanda wannan majalisar daya ne daga cikin cibiyoyi masu muhimmanci na wannan tsari na Musulunci, tun farkon nasarar juyin juya halin Musulunci Amurkawa suke tsananin adawa da ita.

Yayin da yake ishara da cewa sakamakon sanya alamun tambaya cikin matsayar da majalisar kiyaye kundin tsarin mulki shi ne tabbatar da rashin ingancin zabubbukan da za a gudanar, Jagoran ya bayyana cewar: a lokacin da aka sanya alamun tambaya kan rashin ingancin zabe, hakan yana nufin majalisar shawarar Musulunci da za a kafa ta hanyar wannan zaben da kuma dokokin da za ta kafa duk za su zamanto marasa inganci Kenan.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Manufar wannan makircin ita ce sanya kasar nan ta zamanto ta rasa majalisa da kuma dokoki, sannan tsawon shekaru hudu masu zuwa za su shagaltar da kwakwalan mutane da wannan lamarin.

Haka nan kuma yayin da yake Magana kan irin mutanen da suke cikin Iran wadanda kuma suke taimakawa makiya din wajen zubar da mutumcin majalisar kiyaye kundin tsarin mulkin, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Mafi yawa daga cikin wadannan mutanen ba su fahimci abin da suke fadi ba, ba za a iya tuhumarsu da ha'inci ba, to amma wajibi ne su fahimci cewa sakamakon wanda baki guda da suke yi da makiya, shi ne kammala wannan bakar aniya ta makiyan.

Har ila yau kuma yayin da yake magana kan cewa daya daga cikin manufofin ma'abota girman kai cikin sanya alamun tambayar da suke yi kan wadannan zabubbuka ita ce hana al'ummar musulmi riko da wannan tsarin demokradiyya na addini maras tamka a matsayin abin koyi, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da matsayi mai girma da majalisar shawarar Musulunci ta ke da shi a kasar Iran inda ya ce: Ta hanyar kafa dokoki, majalisar tana share hanya ne wajen ci gaban ayyukan gwamnati. A saboda haka zaban ‘yan majalisar da suka dace cikin basira da sanin ya kamata wani lamari ne mai tasirin gaske a fagen ciyar da kasar nan gaba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewar: Matukar dai majalisa tana son ganin jin dadin al'umma, tabbatar da adalci na zamantakewa, karfafa tattalin arziki da ci gaban ilimi da fasaha da ‘yancin kai da daukaka ta kasa, to kuwa za ta zamanto mai share fagen isa ga hakan ne. Amma idan majalisa ta zamanto mai tsoron kasashen Yammaci da Amurka, sannan kuma wacce take son tabbatar da iko da almubazzaranci, to kuwa za ta share fagen hakan ne da kuma shiryar da kasar nan zuwa ga tafarkin koma baya.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da maganar marigayi Imam Khumaini (r.a) da ke cewa majalisa ita ce a saman dukkanin lamurra, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Abin nufi da wannan magana shi ne ba shi ne matakan gudanarwa da ake bi ba, face dai jaddada irin matsayi mai muhimmanci da majalisar take da shi wajen ayyana mahanga da kuma tafarkin da kasa za ta bi.

A ci gaba da jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da irin matsayi mai muhimmanci da majalisar kwararru ta jagoranci take da shi a tsarin Musulunci na Iran inda ya ce: Matsayin majalisar kwararru ta jagoranci yana cikin irin rawar da take takawa ne wajen zaban jagoran juyin juya halin Musulunci a matsayinsa na mai ayyana siyasa da tafarkin tsarin Musuluncin. A saboda haka zaben ‘yan wannan majalisar, wani lamari ne mai muhimmancin gaske.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Matukar ‘yan majalisar kwararru suka zamanto masu riko da tafarkin juyin juya halin Musulunci, suka zamanto masu kaunar al'umma, masu masaniya da fahimtar makirce-makircen makiya da kuma tsayin daka wajen tinkarar wadannan makirce-makirce, to kuwa matsayar da za su dauka za su kasance sun yi daidai da hakan ne. Amma matukar suka zamanto ba haka ba, to kuwa wani abin na daban za su yi.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da kokarin makiya na bata sunan majalisar kwararrun, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: wannan shi ne dalilin da ya sanya na ke jadada wajibcin amfani da basira da fahimta yayin zaben, don su sami damar aikata abin da ya saba wa manufar makiya.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya sake kiran al'ummar Iran zuwa ga fitowa kwansu da kwarkwatansu yayin zabe da kuma ba da kariya ga tsarin Musulunci da ‘yanci da daukakar kasa da al'umma, bugu da taka tsantsan dangane da makircin ma'abota girman kai wadanda suke karkashin ikon sahyoniyawan duniya. Jagoran ya bayyana cewar: siyasar Amurka da mafi yawa daga cikin gwamnatocin Turai suna karkashin ikon wannan cibiya ce (ta sahyoniyawa) wanda aikin Amurka cikin lamarin nukiliya ma lamari ne da ke tabbatar da hakan.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Bayan tattaunawa mai tsawo ta nukiliya da kuma yarjejeniyar aka cimma, sai ga shi a kwanakin baya-bayan nan wani jami'in Amurka yana fadin cewa za mu yi abin da manyan ‘yan kasuwan duniya ba za su iya tafiya Iran su zuba jari ba.

Yayin da yake ishara da cewa irin wadannan maganganu wata alama ce da take nuni da irin gagarumar kiyayyar da Amurka take yi da al'ummar Iran, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Daya daga cikin manufofin mutanen da tsawon shekaru biyun da suka gabata suke ta tattaunawa ta nukiliya, kuma lalle sun yi gagarumin aiki, ita ce karfafa tattalin arziki ta hanyar shigo da masu zuba jari daga waje. To amma sai ga shi Amurkawa suna kokarin hana faruwar hakan.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Wannan ita ce ma'ana da kuma dalilan da suka sanya a lokuta da dama nake fadin cewa Amurkawa dai ba abin yarda ba ne.

Har ila yau kuma yayin da yake ishara da damuwar da ‘yan siyasar Amurka suke nunawa dangane da taken "Allah Ya La'anci Amurka" da ake rerawa yayin jerin gwano a Iran, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Yayin da kuke aikata irin wannan aikin sannan kuma tarihinku na da da na yanzu yake ishara da kiyayyarku (ga al'ummar Iran), shin me kuke tsammani daga wajen al'ummar Iran?

Jagoran ya ci gaba da cewa: Koda yake a yayin ganawa ta sirri su kan sake fuska, da mika hannu da fadin maganganu masu dadi, wadanda irin hakan suna da alaka ne da ganawa ta diplomasiyya, wanda hakan ba shi da wani tasiri cikin hakikanin lamarin.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewar: Hakikanin lamarin shi ne cewa bayan gama tattaunawar nukiliya da rufe wannan shafin, amma a halin yanzu suna fadin cewa ba za mu taba bari ba, suna ma magana kan wasu sabbin takunkumin.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Wannan shi ne hakikanin Amurka. Don haka babu yadda za a yi mu rufe idonmu kan irin wannan kiyayyar.

Jagoran ya kirayi al'ummar Iran da cewa: Ya ku al'ummar Iran, irin wadannan mutanen su ne makiyanku. A saboda haka wajibi ne ku farka sannan kuma ku yi taka tsantsan.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Hanyar magance matsalolin da kasar nan take fuskanta ita ce farkawar al'umma, kiyaye manufofi da Imani cikin al'umma, amfani da matasa masu Imani da karfin gwiwa wajen ciyar da kasar nan gaba a fagen tattalin arziki, ilimi da kuma yanayin gudanarwa.

Har ila yau kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada wajibcin hadin kai da baki guda wajen kare juyin juya halin Musulunci da koyarwarsa.

Daga karshe dai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Da yardar Allah, wata rana za ta zo da matasan kasar nan za su ga cewa Amurka kai da ma wacce take sama da Amurka ba za su iya yin wani abu wa al'ummar Iran ba.

Kafin jawabin Jagoran, sai da Ayatullah Mujtahid Shabastari, wakilin Jagora a lardin Azarbaijan ta Gabas sannan kuma limamin Juma'ar Tabriz ya gabatar da jawabinsa inda yayi ishara da irin rawar da mutanen lardin Azarbaijan suka taka yayin juyin juya halin Musulunci, da kuma aniyar da suke da ita na ci gaba da hakan da kuma fitowa yayin zaben da za a gudanar a nan gaba a Iran.

3476409

captcha