IQNA

16:59 - February 28, 2016
Lambar Labari: 3480188
Bangaren kasa da kasa, kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya mince da cewa mahukuntan kasar bahrains una zaluntar val’ummar kasar.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Mir’atul Bahrain cewa, kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya kai matsayin cewa ya amince da batun da ake na cin zarafin yan adam a kasar Bahrain babu kakakutawa.

A cikin wani rahoto wanda kwamitin ya fitar bayan da ya harhada shi ta hanyar jin ta bakin mutane da daman a kasar da aka zalunta kuma a cutar da su aka gallaza musu ba tare da hakkinsu ba.

Daga mutanen akwai Sheikh Mausam Salman, wanda daya ne daga cikin malaman addini a kasar wanda aka kame shi kuma ake ci gab ada tsare shi ba tare da wani laifi ba, wanda an ji ta bakin mutane da dama kan batunsa.

Haka nan kuma akwai mutane wadanda suka hada da malaman addini, da kanann yara da mata wadanda ake tsare da su bisa zalunci da kuma hana su fadin albarkacin bakinsu.

Kamar yadda kuma akwai masu rajin kare hakkin bila dama da dama da ake tsare da su saboda nuna rashin gamsuwa da suke kana bin da ake cin zarafin al’ummar kasar da kuma gallaza musu saboda dalilai na siyasa da bangaranci.

Baya ga hakan kuma, ana azabtar da mutane domin su amince da wasu laifuka da ake jinginawa gare su, daga cikinsu akwai Muhammad Ramadan, da Musa Hussain, wadanda aka azabtar da su domin su amsa laifi, kuma aka yanke hukuncin kisa akansu.

Irin wannan bakin mulki na zalunci shi ne ya shafi Sheikh Ali Salman daya daga cikin masu fafutuka a kasar, wanda yake hannu tun kimanin shekara guda da rabi yana tsare saboda dalilai na siyasa.

3478913

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: