IQNA

Kasashen Yankin Tekun Fasha Sun Saka Hizbullah A Cikin ‘Yan Ta’adda

23:45 - March 02, 2016
Lambar Labari: 3480197
Bangaren kasa da kasa, kasashen larabawan yankin tekun fasha da ke da hannu wajen kafa kungiyoyin y’yan ta’adda da suka addabi duniya da kuma yanking abas tsakiya sun saka Hizbullah cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na Sky News Arabic cewa, wadannan kasashe sun dauki wannan mataki ne a yau kamar yadda kuma suka sanar da hakan a yau.

Abdullatif Bin Rashid Al-zayani babban sakataren kungiyar ya bayyana a cikin wani bayani da ya fitar a yau cewa, sun dauki wannan mataki ne saboda abin da ya kira hannu da kungiyar Hizbullah take da shi wajen yin barazana ga tsaron kasashen larabawa.

Bayanin ay ci gaba da cewa wadanna kasashen sun yi hakan ne saboda kungiyar Hizbullah baya ga shigar shugula da take acikin kasashen larabawan yankin tekun fasha, kuma tana horar da wasu mutanen yankin domin hada bama-bamai da kuma kai hare-hare.

Wannan mataki dai ya zo ne a daidai lokacin da kungiyar Hizbullah ta zama babban karfen kafa na hana wadannan kasashe tare da kawayensu na turai da kuma Isra’ila wajen aiwatar da manufarsu wajen rusa kasashen Syria da kuma Lebanon kamar yadda suka shirya.

Tun bayan da wadannan kasashe suka fara tura yan ta’adda a Syria a da nufin kifar da gwamnatin kasar tare da mayar da kasar wata babbar tungar yan ta’adda ta duniya, suka bayyana kiyayayrsu ga kungiyar Hizbullah, wadda ta ce yana goyon bayan halastacciyar gwamnati a kasar Syria, kuna daga bisani ta shiga yakin domin taimaka ma gwamnati da sauran al’umma wajen tunkarar wannans hiri na yahudawa tare da kasashen larabawan yankin tekun fasha.


3480057

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :