IQNA

An Bayyana Trump A Matsayin Mutumin Mafi Gaba Da Msulinci Na Shekara

23:49 - March 06, 2016
Lambar Labari: 3480207
Bangaren kasa da kasa, wata kungiyar kare hakkokin muslmi a kasar Birtaniya ta zabi Donal Trump a matsayin mutumin da ya fi gaba da mslnci an shekara ta 2016.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya nakalto daga jaridar Time ta kasar Birtaniya cewa, Donal Trump dan takarar shugabancin kasar Amurka a karkashin inuwar jam’iyyar Republican ya samu matsayi na daya wajen kin muslunci na shekara ta 2016 daga kungiyar kare hakkokin muslmi a birnin landan.

Masud Shajareh shugaban wannan kungiyar shi ne wanda ya sanar da hakan a wani shiri da kungiyar take shiryawa amatsayin wasan kwakwayo, wanda ya samu karbuwa daga musulmin kasar.

Daga cikin yan takarar bneman wannan mukami na shekara ta 2016 akwai Geert Wilders dan kasar Holand wnda ya shahara wajen kin addinin muslunci.

Shi Firayi ministan kasar Brtaniya David Cameron ya samu nasa rabon a kokarin da yake na tilastamuauslmi mazauna Birtaniya koyon harshen turancin Ingilishi, inda aka bayyana hakana matsayin wani nayi nanuna kyama da cin zarafin musulmi a wannan shekara.

Wannan cibiya dai ta yi suna akasar wajen shiga gab adomin kare hakkkokin musulmi a kasar baki daya.

3481130

captcha