IQNA

An Girmama Wadanda Suka Gudanar da Gasar Kr’ani Masu Nakasa A UAE

23:32 - March 10, 2016
Lambar Labari: 3480218
Bangaren kasa da kasa, an girmama wadanda suka gudanar da gasar karatun kr’ani mai tsarki ta masu nakasa a Ra’asul Khima da ke kasar UAE.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Albayan cewa, a jiya an girmama wadanda suka gudanar da gasar karatun kr’ani mai tsarki ta masu nakasa a Ra’asul Khima da ke kasar hadaddiyar daular larabawa.

An gudanar da taron girmama wadanda suka nuna kwazo tare da halartar Jabir Ali Mansur mamba na hukumar kula da ayyukan kur’ani ta kasa daga yankin Ra’asul Khaima, kamar yadda kuma mahaifan wadanda aka girmama sun samu halarta.

An kasa bangarorin gasar biyu na maza da mata, an zabi maza 45 da kuma mata su 45 da aka girma bayan da suka nuna kwazo a wanann gasa wadda it ace karo na sha shida da ake gudanar da ita.

Dukkanin wadanda suka gudanart da addinsu ya kai 157 kuma an zabo su daga wurare 10 da ake kula da matsaloli na nakasa a kasa a wannan gari, daga karshe kuma aka zabi 90 daga cikinsu domin girmama su.

Wannan cibiya ta Ra’asul khaima da ke kula da shirya wanna gasa tana da alaka da ma’aikatar kula da harkokin zamantakewa a Ajman da kuma Dubai, wadanda dukkaninsu bababr ma’aikatar ta kasa c eke daukar nauyin ayyukansu a wannan bangare.

3482161

captcha