IQNA

Gargadi Kan Raunana Tunani Da Juyin A Cibiyoyin Ilminin Addini

23:22 - March 16, 2016
Lambar Labari: 3480236
Bangaren siyasa, a lokacn da yake ganawa da wakilan dalibai na hauzar Qom jagoran juyin juya halin muslunci ya yi gargadi kan cewa wajibi ne cibiyar ilimin addini ta ci gaba da kasancewa wurin ci gaba da samar da tunanin juyi wanda zai zama babban abin dogaro ga makomar juyin Islama.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jagora cewa, a safiyar Talata ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da membobin majalisar wakilan dalibai da malaman makarantar Hauza ta Qum, inda yayin da yake bayanin irin gagarumar rawar da makarantar Hauzar Qum ta taka wajen nasarar juyin juya halin Musulunci, Jagoran yayi ishara da kokarin da wasu suke yi na cire ruhin juyin juya hali daga makarantun Hauzar inda ya ce: Wajibi ne makarantar Hauzar Qum ta ci gaba da zamanta a matsayin ‘wata cibiya da makaranta ma'abociyar juyi da riko da koyarwarsa'. Cimma hakan kuwa yana bukatar tunani da kuma tsare-tsare masu kyau.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya fara jawabin nasa ne da share fage dangane da tasirin makarantar Hauzar Qum wajen samar da nasarar juyin juya halin Musulunci da kuma ci gaba da wanzuwarsa inda ya ce: Akwai wasu cibiyoyi guda biyu da suka taka gagarumar rawa wajen tsari da kuma nasarar juyin juya halin Musulunci, su ne kuwa: 1- Jami'a da kuma na 2- Makarantar Hauza.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da samuwar gwagwarmaya ta ‘yan jami'a a bangarori daban-daban na duniya saboda irin yanayin jami'oi da kuma masaniyar da daliban jami'a suke da ita kan lamurran yau da kullum, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: An samu gwagwarmayar daliban jami'a a Iran, shin a lokacin gwagwarmayar Musulunci ne ko kuma kafin nan, to amma sakamakon takaita tasirin hakan da aka yi, babu wani lokaci da ta zama wani sauyi da juyin juya hali a kasar nan.

Jagoran ya bayyana cewar yunkuri da gwagwarmayar jami'oi ta yi tasiri cikin nasarar juyin juya halin Musulunci ne sakamakon kasantuwar tushensa na asali wanda shi ne gwagwarmayar malaman addini. Daga nan sai ya ce: Mu dai muna jinjinawa da kuma girmama gwagwarmayar daliban jami'oi, to amma idan da ba don kasantuwar gwagwarmayar malamai ba, ko shakka babu da (gwagwarmayar ta su) ta takaita ne da cikin jami'a kawai kuma da a wajen za ta kare.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana "yaduwa ta gama gari da kuma yin tasiri" a matsayin wasu siffofi biyu da yunkurin malamai a yayin juyin juya halin Musulunci ya kebanta da su, inda ya ce: Makarantar Hauzar Qum ne dai ta kumshi bangarori biyu ne, su ne kuwa "marja'iyya da dalibai", wanda marigayi Imam Khumaini, yardar Allah ta tabbata a gare shi, a matsayinsa na bangaren marja'iyya ya kan fitar da sanarwa da kuma yin jawabai, to amma bangaren da isar da jawabai da kuma mahangar marigayi Imam, yardar Allah ta tabbata a gare shi, zuwa ga mutane da sauran yankuna na nesa, su ne malamai da daliban hauza.

Ayatullah Khamenei ya jaddada cewar: Idan da ba don makarantar Hauzar Qum ba, mai yiyuwa ne da yunkurin marigayi Imam Khumaini (r.a) bai kai ga nasara ba. Hakan kuwa wani lamari ne da ke nuni da tasiri da kuma rawar da makarantar Hauzar Qum ta taka wajen kafawa da kuma ci gaban juyin juya halin Musulunci.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Karfin da ya fito da mutane kan tituna da kuma gudanar da zanga-zangar miliyoyin mutane, shi ne dai tasirin daliban makarantun addini wadanda suka isar da tunani da kuma niyyar marigayi Imam (r.a) zuwa bangarori daban-daban na kasar nan.

Haka nan kuma yayin da yake bayyana cewar makarantar Hauzar Qum ta kasance wata gada da take kulla alaka tsakanin marigayi Imam Khumaini (r.a) da kafa juyin juya halin Musulunci, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Sakamakon irin wannan gagarumar rawa kuma maras tamka da makarantar Hauzar Qum ta taka wajen nasarar juyin juya halin Musulunci, hakan ne ya sanya a hakan yanzu aka kirkiro da wani shiri da makirci na kawar da runin juyin juya hali a cikin makarantun Hauza.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Matukar dai muna son tsarin Musulunci ya ci gaba da zama ‘mai riko da Musulunci da koyarwar juyi', to kuwa wajibi ne mu kiyaye makarantar Hauza ta ci gaba da zama ma'abociyar ruhin juyin juya hali. Don kuwa matukar dai makarantar Hauza ta rasa ruhin juyin juya hali, to kuwa tsarin Musulunci na cikin hatsarin kaucewa daga tafarkin juyin juya halin Musulunci.

Har ila yau yayin da yake jaddada cewar duk wani kokari na kawar da ruhin juyin juya hali a cikin makarantar Hauza wani lamari ne mai hatsarin gaske inda ya ce: Wajibi ne a yi fada da wannan shiri ta hanyar tunani da tsari da ke ciki da hikima, don tabbatar da an kiyaye makarantar Hauzar ta ci gaba da zama wata hauza da kuma cibiyar ma'abociyar juyi, da kuma ganin an fadada tunani da kuma koyarwar juyi.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da hanyoyin da (makiya) suke bi wajen fada da juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: A wani lokaci a fili suke nuna adawarsu da tushen juyin juya halin Musulunci, amma a wani lokacin kuma ba kai tsaye suke adawa da tushe da kuma koyarwar juyin juya halin Musuluncin ba. A saboda haka wajibi ne a yi taka tsantsan a wannan bangaren. A saboda haka ne ma nake yawaiwa jaddada wajibcin taka tsantsan dangane da ma'abota girman kai da kuma Amurka.

Ayatullah Khamenei ya bayyana tsayin dakan da Iran ta yi wajen tinkarar tsarin zalunci na duniya a matsayin babban dalilan da ya sanya ‘yan mulkin mallaka suke adawa da kuma kiyayya da Iran inda ya ce: Idan da ba don wannan tsayin dakan ba, to kuwa da ‘yan mulkin mallaka ba su yi adawa da ku ba ko da kuwa wani irin suna ko tsari kuke da shi.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana adawa da tushe da kuma koyarwar marigayi Imam Khumaini bugu da kari kan basira da tsayin dakan al'ummar Iran a matsayin wata hanya wacce ba ta kai tsaye ba da makiyan suke adawa da juyin juya halin Musulunci da kuma gwamnatin Musulunci. Daga nan sai ya ce: Ma'ana ta hakika ta fada ta siyasa da farfaganda da tushe da kuma koyarwar marigayi Imam Khumaini, yardar Allah ta tabbata a gare shi, shi ne kiyayya da Musulunci na siyasa da kuma Musulunci na hakika wanda aka tabbatar da shi a hukumance karon farko tun bayan bayyanar Musulunci a Iran.

Haka nan kuma yayin da yake bayanin hanyar fada da wannan yunkuri na raunana tunani da ruhin juyin juya hali a makarantun Hauza, Jagoran cewa yayi: Jami'an makarantun Hauza musamman majalisar wakilan dalibai makarantar Hauzar Qum za su iya taka gagarumar rawa a wannan fagen ta hanyar fadada tsare-tsaren da ake da su da kuma kulla alaka da tushen makarantar Hauzar, kafa kungiyoyi na tunani don gano hanyoyin da suka dace wajen yadawa da kuma kwadaitar da tunani irin na juyi, bugu da kari kuma kan gano matsaloli da shubuhohin da ake sanya su cikin kwakwalan dalibai da kuma hanyoyin magance su.

Ayatullah Khamenei ya bayyana samar da majalisar wakilan daliban Hauzar a matsayin wani lamari mai kyau, wanda ya zama wajibi ne a karfafa ta da kuma tabbatar da ita ta hanyar dokoki da kuma matsayi da kuma abin da ta kumsa.

Daga karshe dai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Duk kuwa da kasantuwar wasu abubuwa da matsaloli a nan da can, to amma dai mahanga ta gaba daya da kuma tafiya ta gaba daya ta kasa yanayi ne mai kyau sannan kuma an kama hanyar ci gaba. Cikin yarda da taimakon Allah, makomar kasar nan wata makoma ce mai kyau a dukkanin fagage.

Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musulunci, sai da Hujjatul Islam wal Muslimin Husaini Nejad, shugaban majalisar wakilan dalibai da malaman makarantar Hauzar Qum, ya gabatar da rahoto dangane da tsare-tsare da kuma ayyukan majalisar ta su.

3483511

captcha