IQNA

23:39 - March 17, 2016
Lambar Labari: 3480239
Bangaren kasa da kasa, jaridar De Velt ta kasar Jamus ta bayar da rahoto kan aikin ginin masallaci mafi girma a kasar Algeria.

Kamfanin dillancin labaran Iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Misr Ikhbariyyah cewa, jaridar De Velt ta kasar Jamus ta bayar da rahoto kan halin da ake ciki dangane da aikin ginin masallaci mafi girma a kasar Algeria, da kuma matsalolin da yake fuskanta sakamakon matsaloli tattalin arziki da kasar take fuskanta.

Ya zo a cikin rahoton cewa, aikin wannan masallaci zai kasance ne da fadin mita dubu 374, yayin da tsawon hasumiyrsa zai kai mita 265.

Tsawon tulluwarsa kumabayan kammala ginin zai kai mita 45, yayin da kuma mutanen da zai dauka acikinsa zai kai mutane dbu 35.

Yugen Angel dan kasar Jamus shi ne injiniyan da ya tsara taswirar wannan masallaci, kuma yana ci gaba da aiki a kanta.

Wannan aiki dai ana ci gaba da gudanar da shi, to amma saboda matsaloli na tattalin arziki da suka hada rashin ayyukan yi a tsakanin matasa, da kuma faduwar farashin mai a duniya, ya sanya aikin yana fuskantar matsaloli.

Jaridar ta ce tana fatan kasar Algeria za ta yi iyakacin kokarinta domin ganin an samu nasarar kammala wannan aiki, duk kuwa da cewa zai ci biliyoyin kudade na yuro.

3484035

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: