IQNA

23:54 - March 18, 2016
Lambar Labari: 3480242
Bangaren kasa da kasa, a wani aiki na hadin gwaiwa da jami’an tsaron kasar Tunisia suka gudanar a garin Qirwan sun samu sa’ar cafke wasu gungun yan ta’adda.

Kamfanin dillanicn labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Aljaridah Tnis cewa, jami’an tsaron sun kame yan ta’adda kimanin arba’in da yan kai dukkanin yan takfiriyya da suke shirin kai hari na ta’addanci a kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa ana tuhumar mutane 48 da shiga cikin wannan gngu na ‘yan ta’adda dake daukar nauyinsu daga kasshen larabawa, inda aka cafke 20 daga cikinsu, kuma ana ci gaba da neman sauran.

Tun kafin wannan lokacin dai mahukunta akasar Tunisia sun sanar da fara gudanar da ayyukan na hadin gwiwa atsakanin jami’an tsaro somin fuskantar yan ta’adda da suke barazana ga zaman lafiyar kasar.

3484090

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: