IQNA

A Sakon Norouz Jagora Ya Bayyana Sabuwar Shekara:
21:29 - March 20, 2016
Lambar Labari: 3480247
Bangaren siyasa, A cikin sakonsa na sabuwar shekara ta 1395 hijira shamsiyya, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya sanya wa sabuwar shekarar ta bana sunan shekarar"Daukar Mataki Da Aiki A Fagen Tattalin Arzikin Dogaro Da Kai".

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya nakalto daga shafin jagora cewa, a sakonsa na sabuwar shekara jagora ya fara da wannan addu’a Ya Mai sassauya zukata da idanuwa, Ya Mai jujjuya dare da rana, Ya Mai sauya karfi da yanayi. Ka sauya yanayinmu zuwa ga mafi kyawun yanayi.

Amincin Allah ya tabbata ga Siddiqatut Tahira, Fatima al-Mardhiyyah, ‘yar Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayensa. Haka nan amincin Allah ya tabbata ga Waliyin Allah mai girma, rayukanmu su zamanto fansa a gare shi sannan kuma Ya gaggauta bayyanarsa.

Ina mika sakon taya murnar Idin Nourouz ga dukkanin al'ummar Iran da sauran Iraniyawa da suke sauran yankuna na duniya. Ina taya ku murnar wannan idi, Ya Ku ‘yan'uwana ‘yan kasa, musamman iyalan shahidai masu girma da daukaka, da sojojin da suka sami raunuka a wajajen yaki da iyalansu masu girma, haka nan ga dukkanin sojoji masu sadaukarwa. Kamar yadda kuma muke jinjinawa shahidanmu masu girma da kuma marigayi Imam Khumaini abin kaunarmu.

Wannan sabuwar shekarar dai - wato shekarar 1395- farkonta haka nan karshenta, dukkaninsu sun sami albarkacin sunan mai grima Nana Fatima al-Zahra (amincin Allah ya tabbata a gare ta). Farkon shekarar yayi daidai da ranakun haihuwar wannan babbar baiwar Allah a watannin hijira kamariyya, haka ma karshen shekarar. A saboda haka muna fatan insha Allahu wannan shekara ta 1395, albarkacin Nata Fatima, za ta zamanto shekara mai cike da albarkoki ga al'ummar Iran sannan kuma za mu dau darussa daga irin kusaci da Allah da take da shi da kuma irin maganganu da kuma rayuwarta da kuma amfanuwa da hakan.

Shekarar da ta kare - wato 1394 - kamar sauran shekarun da suka gabata, shekara ce da take cike da abubuwan faranta rai da kuma masu bakanta rai, haka nan da ci gaba da kuma koma baya; haka daman rayuwa take; kama daga abin bakin cikin da ya faru a Mina (wajen jifar Shaidan yayin aikin hajji) har zuwa ga abubuwa masu faranta rai irin su jerin gwanon ranar 22 ga watan Bahman (don tunawa da zagayowar ranar da aka samu nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran) da zaben 17 ga watan Esfand (26 Fabrairu); haka nan da fara aiwatar da yarjejeniyar nukiliya da irin fatan da ake da shi bugu da kari kuma kan wasu damuwa da dardar din da ke cikin hakan; dukkanin wadannan suna daga cikin abubuwan da suka faru a shekarar da ta gabatan. Haka lamarin ya kasance a dukkanin shekarun da suka gabata.

Shekaru da kuma ranakun rayuwar dan'adam cike suke da dama da kuma barazana da kalubale. A saboda haka wajibi ne mu zamanto masu amfanuwa da damar da muka samu, sannan mu kuma mayar da barazanar da muke fuskanta zuwa ga wata dama. Yanzu dai ga shekarar 1395 a gabanmu. A wannan shekarar ma kamar yadda aka saba, akwai dama da kuma barazana da kalubale. A saboda haka wajibi ne kowanenmu yayi kokarinsa wajen ganin mun amfana da damar da muke da su amfanuwa ta hakika, don kasar nan ta samu ci gaba tsawon wannan shekarar, tun daga farkonta har zuwa karshe.

Lalle akwai kyakkyawar fata a wannan shekara ta 1395. Idan mutum ya kalli yanayin kasar nan a yanayi na gaba daya, to lalle zai ga cewa akwai fata da yawa. Koda yake wajibi ne a yi kokari da hobbasa wajen ganin an cimma wadannan fatan. Wajibi ne a yi aiki ba dare ba rana, a yi aiki ba kama hannun yaro. Asalin lamarin dai shi ne cewa wajibi ne al'ummar Iran su yi aiki wajen ganin sun fitar da kansu daga da'irar barazanar makiya da kuma cutarwarsu. Wajibi ne mu yunkura da tinkarar barazanar makiya ta yadda za mu tseratar da kanmu daga cutarwarsu. Mu kawar da dukkanin cutarwarsu daga kawukanmu.

A tunanina batun karfafa tattalin arziki shi ne a kan gaban komai. Wato a yayin da mutum ya kalli matsalolin da ake da su, zai ga cewa matsalar tattalin arzikin ita ce babbar matsalar da take kan gaba wacce take bukatar a magance ta cikin gaggawa. Idan har cikin yarda da taimakon Ubangiji, al'umma da kuma gwamnati da sauran jami'an bangarori daban-daban suka samu nasarar aikata ayyukan da suka dace a fagen tattalin arziki sannan kuma a daidai lokacin da ake bukata, to fatan da muke da shi shi ne cewa za a samu damar yin tasiri da magance sauran matsalolin da ake da su irin su matsalar zamantakewa, matsalar kyawawan halaye da matsalar al'adu da sauransu.

Dangane da batun tattalin arziki, abin da ke da muhimmanci kuma na asali shi ne batun samar da kayayyakin da ake bukata a cikin gida; batun samar da aikin yi da kawar da rashin aikin yi; batun yunkuri da karfafa tattalin arziki da fada da koma bayan tattalin arziki; wadannan matsaloli ne da al'ummarmu suke fuskanta. Wadannan matsaloli ne da al'ummarmu suke ji a jikinsu kuma suke bukatar a magance musu su. Kuma kididdiga da maganganun su kansu jami'an gwamnati suna nuni da cewa lalle haka lamarin yake.

Matukar muna son magance matsalar koma bayan da ake fuskanta, matsalar kayayyakin da ake samarwa a cikin gida, matukar muna son magance matsalar rashin aikin yi, matukar muna son kawar da matsalar tsadar kayayyaki, to kuwa maganin dukkanin wadannan matsalolin suna cikin tsarin siyasar tattalin arziki na gwagwarmaya da dogaro da kai ne. Tattalin arzikin dogaro da kai ya kumshi dukkanin wadannan abubuwan. Ana iya kawar da matsalar rashin aikin yi ta hanyar riko da tattalin arzikin dogaro da kai, ana iya magance matsalar koma baya, haka nan da matsalar tsadar rayuwa, haka nan ana iya tsayin daka da tinkarar barazanar makiya; ana iya samar da dama masu yawa ga kasar nan da kuma amfanuwa da wadannan damar; to amma da sharadin za a yi aiki tukuru wajen tabbatar da wannan siyasa ta tattalin arziki na dogaro da kai.

Rahotanni da bayanan da ‘yan'uwanmu jami'an gwamnati suka aiko min, suna nuni da cewa an aiwatar da ayyuka masu yawa a wannan bangaren; koda yake wadannan ayyukan, ayyuka ne na share fage; ayyukan da aka gudanar a bangarori daban-daban da suka shafi umurni ga cibiyoyi daban-daban na gwamnati; dukkaninsu ayyuka ne na share fage; to amma abin da ya zama wajibi a ci gaba da shi, shi ne daukar mataki da kuma aiwatar da hakan a aikace, mutane su ga sakamakon hakan a kas. Wannan shi ne nauyin da ke wuyanmu; wanda insha Allah a jawabin da zan yi zan yi karin bayani sosai ga al'ummarmu.

A saboda haka taken da na zaba wa wannan shekarar shi ne"Daukar Mataki Da Aiki A Fagen Tattalin Arzikin Dogaro Da Kai". Wannan ita ce mikakkiyar hanya kuma fitacciya zuwa ga abubuwan da muke bukata. Tabbas ba wai muna cewa wadannan daukar matakai da kuma aiki a aikace za su magance dukkanin matsalolin da ake da su cikin shekara guda ba ne; to amma ko shakka babu matukar aka aikata hakan yadda ya dace, to kuwa a karshen shekarar nan za mu ga tasiri da kuma alamun hakan. A saboda haka ina mika godiya ta ga dukkanin mutanen da suka yi kokari a wannan fagen.

Ina sake mika gaisuwa ta da kuma taya murna ga al'ummarmu masu girma, sannan kuma ina rokon Allah Madaukakin Sarki da yayi salati da tabbatar da aminci ga Annabi Muhammadu da Alayen Muhammadu haka nan kuma ga mai girma baqiyatullah rayukanmu su zamanto fansa a gare shi.

3484210


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: