IQNA

21:33 - March 20, 2016
Lambar Labari: 3480248
Bangaren kasa da kasa, an bude wata mujalla mai suna mu’jizar kur’ani mai tsarki a kasar tare da daimakon babbar cibiyar kula da mujizar kur’ani ta duniya.

Kamfanin dillanicn labaran Iqna ya habarta cewa ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na Yaum Sabe cewa, a yau an kaddamar da mujjar mai suna mu’jizar kur’ani mai tsarki a kasar tare da halatar Ali Fu’ad Mukhaimir da kuma Abdullah Musleh shugaban babbar cibiyar kula da mujizar kur’ani ta duniya wanda aka yi a birnin Alkahira.

Musleh ya bayyana a wajen taron cewa, mujizar kur’ani mai tsarki da sunnar manzon Allah (SAW) babban dalili ne da ke tabbatar da gaskiyarsu.

Shi ma a nasa bangaren Ali Fu’ad a lokacin da yake da gabatar da nasa jawabin ya bayyana cewa, babbar manufar taron ita ce kara fito da matsayin kur’ani mai tsarki da sunnar manzo (SAW) ga al’ummomin duniya baki daya.

Muhammad Haddad babban editan wannan mujja ya bayyana cewa, za su yi amfani da wannan damar wajen bayar da fili ga msana domin su bayyana matsayin kur’ani mai tsarki da koyarwa daidai da yadda manzo ya koyar da al’ummar musumi, domin samn tarbiya bisa koyarwarsa mai tsarki.

3484245

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: