IQNA

Gasar Karatun Kur’ani Mai Tsarki A Birnin Moscow

21:35 - March 20, 2016
Lambar Labari: 3480249
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki mai tsarki tare da halartar manyan malaman muslunci na Rasha a birnin Moscow.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na azertag.az cewa wannan taro na kur’ani za a gudanar da shi ne a babban masallacin juma’a na birnin Moscow tare da halartar masu bayar da fatawa n musuomi a kasar.

An yi has ashen cewa wadanda za su halarci wannan babban taro za su kai mutane dubu 10, a kan haka ya sanya ake gudanar da shirin da ya kamata dukkanin fuskoki da suka kamata, domin bayar da kariya da kuma tabbatar da cewa shirin ya gudana kamar yadda aka tsara shi.

Da farko za a fara gudanar da taro ne, kafin daga bisani kuma ashiga bangaren gasar kur’ani ta yara da shekarnsu ab su wuce 14 ba, wanda kuma da gasar ne za a kammala taron.

Haka nan kuma wasu daga cikin abubuwan da wannan taro zai kunsa har da gasar karatun wakokin larabci da ake ma suna dakin ubangiji, wanda su za su shiga cikin daga wadanda za a baiwa kyautuka na musamman a wurin.

3484256

captcha