IQNA

Jagoran Juyin Juya Hali:

Shawarwari 10 Domin Tabbatar Da Tattalin Arziki Mai Karfi

23:52 - March 21, 2016
Lambar Labari: 3480250
Bangaren siyasa, a lokacin da yake gabatar da jawabi a gaban masu ziyara a hubbaren radwi jagoran juyin juya halin muslunci ya bayyana cewa, makiya suna amfani da kalmomi na rarraba kan al’umma ta hanayar bayyana cewa akwai bangarori biyu na siyasa, y ace doe ne a tabbatar wa makiya cewa juyin juya hali manufarsa guda ce a aikace.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na jagora cewa, a yammacin yau Lahadi ne, wacce ta yi daidai da ranar farko ta sabuwar shekara ta 1395, hijira shamsiyya, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da dubun dubatan al'ummar birnin Mashhad da masu ziyartar hubbaren Imam Ridha (a.s) inda a wani jawabi mai matukar muhimmanci da ya gabatar yayi Karin haske dangane da boyayyiyar manufar Amurka ta yi wasa da hankalin masana da kuma al'ummar Iran don cimma manufofinsu. Har ila yau kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya gabatar da wasu shawarwari guda goma wajen cimma manufofin da aka tsara cikin siyasar tattalin arziki na dogaro da kai da aka gabatar inda ya ce: Wannan tafarki wanda yayi daidai da hankali da kuma koyarwa irin ta juyin juya hali lamari ne da zai kare kasar Iran daga barazana da kuma takunkumi, sannan kuma a karshen shekarar nan gwamnati, bisa goyon bayan sauran bangarori na gwamnati, za ta iya gabatar wa mutane da wani rahoto mai kwantar da hankali dangane da irin ayyukan ci gaban kasa da ta yi.

Yayin da yake gabatar da sakon taya murnar sabuwar shekara ga al'ummar Iran, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar haduwar farkon shekarar da kuma karshenta da ranakun haihuwar Nana Fatima (a.s), wani lamari ne mai cike da albarkoki ga kasar nan.

A ci gaba da jawabin nasa, Ayatullah Khamenei yayi karin haske dangane da take da sunan da aka bai wa sabuwar shekarar wato Shekarar "Daukar Mataki Da Aiki A Fagen Tattalin Arzikin Dogaro Da Kai".

Yayin da yake bayanin cewa an zabi wannan sunan ne bayan tunani da kuma tabbatattun dalilai, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kirayi dukkanin al'ummar Iran musamman matasa zuwa ga tunani cikin wannan sunan inda ya ce: Mai yiyuwa ne wasu su yi tunani da kuma fifita da an ba wa shekarar suna da ke alaka da al'adu ko kuma kyawawan halaye, to amma bisa la'akari da matsalolin da kasar nan take fuskanta, an dauki matakin sa wa shekarar, tamkar shekarun da suka gabata, suna da kuma take irin na tattalin arziki don hakan ya zamanto wani lamari da zai sami kulawa ta al'umma gaba daya.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: An zabi take da sunan wannan shekarar ne bayan tunani da dubi cikin manyan batutuwa da matsalolin da suke damun kasar nan.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: A halin da ake ciki, Amurkawa suna kokarin sanya wa masana da al'ummomin kasar nan wani irin tunani na cewa al'ummar Iran dai suna tsakanin hanyoyi guda biyu, wanda ba su da wata mafita face dai su zabi daya daga cikin biyun.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Hanyoyi guda biyun da suke maganar su ne cewa ko dai al'ummar Iran su amince da abin da Amurka take so ko kuma su ci gaba da zama cikin matsin lambar Amurka da matsalolin da suke faruwa a dalilin hakan.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da "dukiya, hanyoyi na siyasa, kafafen farfaganda masu yawa da kuma makaman da Amurka take da su", Jagoran ya bayyana cewar: Bisa wannan tunani, wajibi ne a yarda da abin da Amurka take so da kuma yin watsi da koyarwa da kuma tafarkin da ake kai da kuma jajayen layin da aka shata da ba za a bari a ketare su ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Irin wannan yanayin shi ne ya faru a yayin yarjejeniyar nukiliya na baya-bayan nan da aka cimma wanda kuma masu tattaunawarmu sun yi iyakacin kokarinsu. Akwai wani lokaci da mai girma ministan harkokin waje ya gaya min cewa: "Mu dai mun gagara kiyaye wasu jajayen layukan da aka shata".

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: "Yarda da siyasar Amurka tana nufin rufe ido da kuma yin watsi da wasu batutuwa da ka yi riko da su a matsayin tushe".

Haka nan yayin da yake bayanin cewa wasu a cikin gidan Iran ma sun yi na'am da wannan tunani mai matukar hatsari na batun hanyoyi biyu (ko dai Iran ta amince da siyasar Amurka ko kuma ta fuskanci matsin lambar Amurka) da kuma kokarin sanya wasu amincewa da hakan, Jagoran cewa yayi: "Wadannan mutanen suna cewa ne Iran tana da dama da yawa da za ta iya amfani da su wajen karfafa tattalin arzikinta, to sai dai cimma yarjejeniyar nukiliya kawai bai wadatar ba, face dai akwai wadansu matsalolin da ke tsakanin Iran da Amurka da wajibi ne al'umma da kuma jami'an Iran su yi kokarin magance su.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana tattaunawa da aiki tare da Amurka dangane da lamurran da suka shafi yankin Yammacin Asiya haka nan da kuma tattaunawa dangane da sabanin da ke tsakanin Iran da Amurka, wato Iran ta yi watsi da tafarkin da take kai da kuma jajayen layukan da ta shata, a matsayin wasu daga cikin irin wadannan abubuwa da wadannan mutane suke magana kansu na cewa wajibi ne a magance su bayan cimma yarjejeniyar nukiliyan.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Wadannan mutane suna cewa ne kamar yadda aka kira yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya da sunan "JCPOA", don haka tattaunawa da Amurka dangane da sauran batutuwa na daban ciki kuwa har da batun kundin tsarin mulki na kasar nan ana iya kiransu da "JCPOA na 2 da na 3 da 4" don a cimma wata yarjejeniya da za ta sanya al'ummar Iran rayuwa cikin sauki da kuma magance musu matsalolinsu.

Jagoran ya ci gaba da cewa: "Hakikanin ma'anar wannan tunani mai matukar hatsari ita ce cewa a hankali a hankali Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi watsi da tushen karfi da tsaronta da kuma sauran batutuwan da ta rike wadanda suka yi daidai da koyarwar tsarin Musulunci irin su goyon bayan ‘yan gwagwarmaya da goyon baya na siyasa da take ba wa al'ummomin Palastinu, Yemen da Bahrain sannan kuma ta sanya mahangarta ta yi daidai da ta Amurka.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: "A bisa wannan tunanin, wajibi ne Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ta zamanto kamar wasu kasashen larabawa, wadanda cikin dukkanin wauta da rashin mafadi suke ci gaba da kusatar haramtacciyar kasar Isra'ila, wanda daga karshe dai za su kai matakin yarda da haramtacciyar kasar sahyoniyawan.

Haka nan yayin da yake ishara da cewa sakamakon yarda da irin wannan tunani shi ne ci gaba da ja da baya da yin watsi da dukkanin abubuwan da aka rika, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: "Matukar muka yi aiki da abin da Amurka take so, to kuwa wajibi ne mu yi watsi da karfin kare kanmu da muke da shi da kuma ci gaba da amsa tambayoyin wuce gona da iri na Amurka daban-daban.

Har ila yau yayin da yake magana kan ihu bayan hari da kuma farfagandar da kafafen watsa labaran kasashen yammaci suke ta yadawa dangane da gwajin makamai masu linzami da Iran ta yi a kwanakin baya kuwa, Jagoran ya bayyana cewar: "A daidai lokacin da Amurkawa, bayan wani lokaci, su kan gudanar da atisayen hadin gwiwa a yankin Tekun Fasha duk kuwa da tazarar dubban kilomitoci da ke tsakaninsu da wajen, to amma sai ga shi suna ta tada jijiyoyin wuya dangane da atisayen da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi a cikin gida da kuma hurumin tsaron kasarta".

Haka nan kuma yayin da yake bayanin cewa amincewa da wannan tunanin zai kara wa Amurka girman kai da kuma neman wuce gona da irinta da kuma ci gaba da tilasta wa Iran ja da baya da kuma watsi da koyarwar da ta rika, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: A ci gaba da hakan, wajibi ne Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta dinga yi wa Amurka bayanin da wani dalili ne ta kirkiro dakarun kare juyin juya hali da kuma dakarun Qudus, me ya sa za a dinga gudanar da siyasar cikin gida bisa koyarwar shari'ar Musulunci, me ya sa dukkanin bangarori uku na gwamnati za su dinga gudanar da ayyukansu karkashin shari'ar Musulunci sannan kuma da wani dalili ne majalisar kiyaye kundin tsarin mulki ba za ta amince da duk wata dokar da ta yi hannun riga da shari'a ba?

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Matukar muka nuna gazawa a gaban Amurka, to kuwa makiyan (Amurka) za su ci gaba da takura mana ta yadda lamarin zai kai matsayin da Jamhuriyar Musulunci za ta zamanto ba komai ba ne face suna na zahiri kawai.

Jagoran ya kara da cewa: Bisa wannan tunani da abin da makiya suke so, matukar dai al'ummar Iran suna son tsira daga sharrin Amurka, to wajibi ne su yi watsi da ma'ana da tafarki na Musulunci da kuma tsaron kasarsu da suka rika.

Bayan bayanan bangarori daban-daban na irin wannan tunanin, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi karin haske dangane da irin cutarwar da Iran za ta fuskanta a wannan bangaren inda yace: Daga cikin abubuwan da za a rufe ido kansu matukar aka amince da wannan tunanin shi ne cewa duk wata yarjejeniyar da aka cimma da Amurka hakan na nufin tilasta wa Iran yarda da wasu abubuwan da wajibi ne ta cika su, duk kuwa da rashin aminci da kuma karya alkawarin da Amurka take yi wanda a halin yanzu ma a fili muke ganin hakan. Wannan shi ne ‘babbar hasara'.

Ayatullah Khamenei ya kawo misalin yarjejeniyar nukiliya da aka cimma a matsayin misali na irin rashin cika alkawarin Amurkan inda ya ce: A cikin wannan yarjejeniyar ma Amurkawa ba su yi aiki da alkawarin da suka dauka ba. Kamar yadda ministan harkokin wajenmu ne ya fadi a rubuce kan sun sanya hannu kan yarjejeniya da alkawurra, amma a aikace kan sun kirkiro wasu hanyoyi na hana aiwatar da abin da aka cimma din.

Jagoran ya ci gaba da cewa: A halin yanzu duk da yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma, amma har ya zuwa yanzu muna fuskantar matsaloli wajen mu'amalolinmu na banki kuma an gagara dawo wa Iran da kudadenta da suke waje. Don kuwa kasashen yammaci da wadanda suke karkashin tasirinsu, suna tsoron Amurka.

Har ila yau kuma yayin da yake jaddada cewa daya daga cikin abubuwan da masu gabatar da wannan batu na hanyoyi biyu suka rufe ido kansu shi ne ‘dalili da kuma tushen kiyayyar da Amurka take yi da al'ummar Iran' Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Bisa la'akari da matsayi mai muhimmancin gaske da Iran take da shi a yankin nan, ga kuma gagaruman albarkatun kasa na man fetur da iskar gas, ga kuma yawan al'umma, ga kwararru da masana da ake da su bugu da kari kan tsohon tarihi da take da shi da ya sanya Iran ta zamanto kasa maras tamka a yankin nan. To amma duk da irin wannan matsayin, amma shekara da shekaru kenan ta kasance karkashin ikon Amurkawa, wanda juyin juya halin Musulunci ne ya ‘yantar da wannan kasar daga irin wannan mulkin kama-karya na Amurka.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Juyin juya halin Musulunci ba wai kawai ya ‘yantar da Iran daga ikon Amurka ba ne, face ma dai ya tabbatar da ruhin gwagwarmaya da tsayin daka wajen tinkarar Amurka a yankin nan kai hatta ma a wajen yankin.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Amurkawa dai suna ganin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayin ummul aba'isin din kashin da siyasarsu ta ‘kafa babbar Gabas ta tsakiya' da kuma tabbatar da ikon gwamnatin sahyoniyawa cikin lamurran yankin nan da kuma koma bayan da suka fuskanta a Yemen, Siriya, Iraki da Palastinu. A saboda haka ne kiyayyar da suke yi da al'ummar Iran wata kiyayya ce mai girma. Ba za su taba daina wannan kiyayyar ba kuwa har sai lokacin da suka sake tabbatar da ikonsu a Iran.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da jawabin nasa ne da bayanin dalilan da suka sanya Iran ta jima tana iko a Iran kana daga baya kuma Amurka ta shigo inda ya ce: Turawan Ingila da na Amurka sun kirkiro wasu garkuwa wadanda ta hanyarsu suka samar da yanayin da za su ci gaba da mulkinsu a Iran. To sai dai juyin juya halin Musulunci ya kawar da wadannan garkuwa da kuma kafa wasu na daban don kare Jamhuriyar Musulunci da kuma manufofin al'ummar Iran.

Jagoran ya ci gaba da cewa: A halin yanzu dai Amurkawa suna bin tafarkin diplomasiyya ne wajen sake gina wadannan garkuwar da aka rusa musu su da kuma kawar da garkuwar juyin juya halin Musuluncin.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Gwamnatin kama karya da dagutanci ta Pahlawi ta zamanto garkuwar Amurka mafi muhimmanci a Iran, to amma juyin juya halin Musulunci ya tumbuke gwamnatin Shah da iko na mutum guda a Iran, sannan kuma ya kafa iko da gwamnati ta mutane a madadinta.

Jagoran ya bayyana sanya tsoron manyan kasashen duniya musamman Amurka a cikin zukatan al'umma a matsayin wata garkuwa da ta share fagen ikon ‘yan mulkin mallaka a Iran inda ya ce: Sabanin lokacin mulkin daguti, a halin yanzu a Jamhuriyar Musulunci babu wani mutum, wanda ya san inda duniya ta sag aba sannan kuma mai riko da koyarwar addini da yake tsoron Amurka.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da cewa a halin yanzu ma mai yiyuwa a samu wasu mutanen da suke tsoron Amurkan, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Tsoron Amurka da gwamnatin dagutu ta Iran take yi, wani lamari ne da yayi daidai da hankali, saboda kuwa ba ta da wata garkuwa da za ta kare ta daga Amurka. To amma a Jamhuriyar Musulunci kan tsoron Amurka ba shi da wata ma'ana kuma ta saba wa hankali, don kuwa Jamhuriyar Musulunci tana da goyon baya da kuma kariya daga wajen al'ummar Iran.

Jagoran ya bayyana sanya rashin yarda da kai da kuma kawar da ruhin dogaro da kai na kasa a matsayin wata hanyar da Amurkawa suke amfani da ita wajen tabbatar da ikonsu inda ya ce: Bayan nasarar juyin juya halin Musulunci, an musaya wannan garkuwa ta ‘yan mulkin mallaka da wata garkuwar ta daban da take nuna wa mutane cewa ‘lalle za mu iya'.

Ayatullah Khamenei ya bayyana ‘kokarin raba addini da siyasa' a matsayin wata garkuwar ta daban da Amurka take amfani da ita wajen tabbatar da ikonta a kasar Iran, inda ya ce: juyin juya halin Musulunci ma ya kawar da wannan garkuwar.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar Amurka yake nufi a lokacin da yake amfani da Kalmar makiya inda ja kunnen al'ummar Iran da su yi taka tsantsan da makircin Amurka a yayin da take sakin fuska a wasu bangarorin inda ya ce: ‘yan siyasar Amurka da ma'aikatar kudin kasar suna ci gaba da tabbatar da takunkumin da suka sanya wa Iran da kuma ci gaba da barazanar kara kakaba wasu takunkumin a daidai lokacin da a fadar White House kuma suna faza tabarmar bikin Norouz da aikewa da sakon Norouz da nuna kaunarsu ga matasanmu.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Dalilin irin wadannan halaye masu harshen damo shi ne cewa har ya zuwa yanzu jami'an Amurka ba su fahimci al'ummar Iran ba, ba su san cewa wadannan al'umma ma'abota fahimta, sun yi kyakkyawar fahimta wa manufofi da kuma boyayyun hanyoyin da makiyan suke bi don cimma manufofinsu ba.

A ci gaba da bayanin irin kiyayya da makirce-makircen da Amurka take kulla wa Iran, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da irin kokari ba dare ba rana da wasu jami'an Amurkan suke yi wajen ganin ba a cimma dan abin da aka cimma a yarjejeniyar nukiliya din ba, wanda yace hakan babbar alama ce da take nuni da irin kiyayyar da Amurka take yi da al'ummar Iran.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: ‘Yan watanni ya rage kafin zaben shugaban kasar Amurka, to amma ‘yan takarar zabe suna ci gaba da rigegeniya da gasa a tsakaninsu wajen fadin muggan maganganu kan Iran, kamar yadda babu wani lamuni kan cewa gwamnatin da za ta zo ma za ta girmama dan abin da aka cimma a yarjejeniyar nukiliyan. Amma duk da haka a duk lokacin da aka yi magana kan kiyayyar Amurka sai wasu a gida su dinga magana.

Ayatullah Khamenei yayi ishara da ‘farfaganda', ‘neman kutsawa' da kuma ‘takunkumi' a matsayin wasu abubuwa guda uku da Amurka take amfani da su wajen neman tabbatar da tasirinta a Iran. Don haka Jagoran ya kirayi jami'an gwamnatin Iran din da su yi iyakacin kokarinsu wajen ganin sun karfafa bangaren tattalin arzikin Iran ta hanyar riko da siyasar tattalin arziki na dogaro da kai wanda yace hakan zai magance irin wadannan matsaloli da barazanar da ake fuskanta din.

3484209

captcha