IQNA

Gasar Kur’ani Mai Tsarki A Kasar Malaziya

23:57 - March 21, 2016
Lambar Labari: 3480252
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasar Malaziya a birnin Potrajaya.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na Bernama cewa, wannan gasa cibiyar yada harkokin addinin muslunci ta Jakim ce ta dauki nauyin shiryata har tsawon kwanaki 6 a jere.

Daga cikin wadanda za su halarci gasar su 30, akwai 14 maza da kuma 14 mata, wadanda suka hada da makaranta da mahardata, wadanda kuma wasu daga cikinsu su taba halartar gasar a lokutan baya.

Duk wanda ya o na daya a wanann gasa, zai zamanto shi ne wanda zai wakilci kasar ta Malazia a gasar Amin ta kasa da kasa, da za a gudanar karo na 57 a kasar.

Abin tuni a na dais hi ne, gasar karatun kur’ani mai tsarki ta duniya da ake gudanarwa a Malazia za ta gudana a cikin wata gobe a bababr cibiyar Potra da ke birnin Kualalampour fadar mulkin kasar.

3484287

captcha