IQNA

23:39 - March 23, 2016
Lambar Labari: 3480258
Bangaren kasa da kasa, an kawo karshen gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki da aka shirya a jami’ar Zaitun ta kasar Tunisia.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bawwabah News cewa, a jiya ne aka kamala gasar karatun kur’ani da kuma harda ta daliban jami’ar Zaitun ta kasar Tunisia, tare da halartar Said Hudud shugaban jami’ar.

Dalibai 30 na jami’ar da ma wasu daga wasu jami’oin da suke da alaka da ta daga sassa na kasar suka gudanar da wannan gasa.

An gudanar da gasar hardar ne a bangaren kur’ani baki daya, da kuma rabinsa yayin da wasu kuma suka gabatar da harda rubu’insa.

Daga karshe dai an bayar da kyautuka namusamman ga daliban da suka nuna kwazo a wannan gasa, musamamn wadanda suka zo matsayi na daya da na biyu da kuma na uku a dukkanin bangarorin gasar.

3484398

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: