IQNA

23:36 - March 28, 2016
Lambar Labari: 3480268
Bangaren kasa da kasa, a cikin watan azumi mai zuwa za a gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarkia kasar Australia.

Kamfanin dillanicn labaran Iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na aiqc.com.au cewa, wannan gasa za agudanar da ita ne a bangarori daban-daban na hardar kur’ani, dukkaninsa da kuma juzuoinsa.

Za a bayar da maki 100 ga duk wanda ya shiga gasar, 70 ga kawon harda, 25, ga kyawon karatu da kiyaye ka’idojinsa, sai kuma maki 5 ga kyawun sauti.

An bayar da wa’adi na rbutun sunaye ga masu bukatar halarta daga nan zuwa kafin azumi.

Babbar manufar wannan gasar dai ita ce karfafa gwiwar musulmi mazauna kasar kan harkokin kur’ani mai tsarki, inda tun a cikin shekara ta 2012 aka gabatar da shawar,kuma aka fara aiwatar da ita a cikin 2014.

Yada koyarwar kur’ani a tsakanin musulmi mazauna wannan kasa ta Australia na daga cikin manufofin wannan gasa, da kuma sanya su su zama masu aiki da koyarwar wannan littafi mai tsarki.

Adadin musulmin kasar Australia ya kai dubu 500, kuma wannan shi ne kimanin kasha 5% na dukkanin adadin mutanen kasar.

3484746

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: