IQNA

Babban Mai Bayar Da Fatawa A Masar Ya Ce Za Su Hada Kai Da ‘Yan Shi’a

23:23 - April 03, 2016
Lambar Labari: 3480287
Bangaren kasa da kasa, Shauki Allam baban mai bayar da fatawa a kasar Masar baki daya ya bayyana cewa za su hada kai da mabiya mazhabar shi’a domin yaki da ta’addanci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alwatan cewa, Shauki Allam baban mai bayar da fatawa a kasar Masar baki daya ya bayyana cewa za su hada kai da mabiya mazhabar shi’a domin samun fahimtar juna tsakanin musulmi.

Ya ci gaba da cewa dukkanin bangarorin addinin muslunci na bkatar hadin kai, da hakan ya hada bangarori na Azhar da kuma mabiya mazhabar shi’a domin tabbatar da cewa an samu hadin kan al’ummar musulmi baki daya.

Babban malamin ya kara da cewa mabiya mazhabar a matsayinsu na babban bangare na wannan addini ya zama wajibi a hada kai da sua cikin dukkanin lamurra da suka shafi al’ummar msuulmi, da hakan ya hada da ya ki da ta’addanci.

Shauki Allam ya ce a shirye ya jagoranci duk wata tattaunawa da za a yi tare da mabiya mazhabar shi’a domin samun hadin kan al’ummar musulmi.

Haka nan kuma ya mayar da martini ga wadanda babban burinsu a kowane lokaci shi ne haifar da rarraba atsakanin al’ummar musumi da suna cewa babu riba gare su a cikin abin da suke yi.

Shauki Allam ya ce babu yadda za a yi a mayar da shi’a saniyar ware a cikin lamarin musulmi, kuma batun yaki da ta’addanci a halin yanzu shi’a su ne kan gaba a dukkanin bangarori.

Inda ya bayar da misali da gwagwarmayar al’ummar kasar Lebanon da kuma Iraki wadanda dukkaninsu yan shi’a da suke yaki da ta’addanci a madaddin al’ummar msuulmi, kamar yadda kuma ya buga misali da fatawar Ayatollah Sistani kan wajabcin hada kai tsakanin musulmi domin yaki da ta’addanci.

3485425

captcha