IQNA

An Bude Gasar Kur’ani Ta Duniya A Kasar Masar

22:18 - April 10, 2016
Lambar Labari: 3480309
Bangaren kasa da kasa, an bude babbar gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta duniya karo na 23 a birnin Sharm Sheikh da ke cikin gundumar Simai a kudancin kasar ta Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bawwabah News cewa, Muhammad Mukhrat Juma’a ministan ma’aikatar kula da harkokin addini, da Khadi Abdulazi ministan wasanni da kuma matasa da kma shugaban kwamitin alakalan gasar kur’ani sheikh Hilmi Jamal da sauransu suna daga cikin mahalarta taron.

Muhamamd Mukhtar Juma’a a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wurin, ya bayyana cewa gudanar da wannan babban taro na duniya a wannan wuri na Sharm Sheikh ya tabbatar da cewa akwai tsaro da zaman lafiya a Masar.

Ya ci gaba da cewa a kowane lokaci muslunci yana kira ne zuwa ga zaman lafiya ta fahimtar juna a tsakanin dukkanin al’ummomi, ba tashin hankali da zubar da jinni da yaki da fitina ba kamar yadda wasu suka dauka.

Hakan kuma ya yi ishara da mas aikata ta’addanci da sunan addinin muslunci da cewa, suna wuce gona da iri a cikin wadannan ayyuka nasu, kuma suna bkatar su dawo kan hanya domin su gane mene ne musulunci da kuma koyarwarsa.

Hakla nan kuma ya yi siahara da matsayin wannan wuri na Sinai ta fiskar addinin muslinci, domin kuwa an ambaci dutsen Tur a cikin kissoshin annabi Musa wanda ya rayu a Masar kamar yadda kuma wasu annabawan na daban sun rayua wanna kasa mai tsohon tarihi, kamar dai yadda kur’ani ya mabata a wurare daban-daban.

Khalid Fu’adah gwamnan lardin na Sinai ya bayyana alokacin da yake gabatar da jawabi cewa, hakika abin da minister ya ambata dangane da matsayin wannan wuri ta fuskancin tarihin duniya da kuma addini mai girma matuka, domin wuri ne wanda yake da alaka da dukkanin addinai da suka safka daga sama.

3487370

captcha