IQNA

Jagoran Juyin Juya Hali:

Karfin Jami’an Soji Jamhuriyar Islama Dole Ne Ya Ci Gaba Da Karuwa

19:23 - April 11, 2016
Lambar Labari: 3480312
Bangaren siyasa, a ganawarsa da manyan jami’an sojin kasa, jagoran juyin juya halin muslunci ya bayyan acewa, babban aikin jami’an soji shi ne tsaron kasa daga barazanar makiya, kuma dole ne karfinsu ya ci gaba da karuwa.
Kamfanin dillanicn labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na jagora cewa, a yau Lahadi ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da manyan kwamandojin dakarun sojin Iran inda ya bayyana cewar daya daga cikin siffofin da dakarun sojin na Iran suka kebanta da shi, shi ne cewa baya da karfi da kumakwarewa ta aikin soji har ila yau kuma sun da riko da addini. Jagoran ya bayyana cewar: Babban aikin dakarun soji a tsarin Jamhuriyar Musulunci shi ne ba da kariya da kuma tabbatar da tsaron kasa. A saboda haka wajibi ne a kowace rana a dinga karfafa irin karfi da kuma kwarewa ta aiki soji da sojojin suke da shi bugu da kari kuma kan bangarren kusaci da Ubangiji da suke da shi.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da cewa a yanayin sojoji a kasashen duniya ya kasu kashi biyu, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: A wasu kasashen, sojoji suna a matsayin wasu gungun masu dauke da makami na jeka na yi ka ne kawai, babban aikinsu shi ne kiyaye gwamnati da tsaron masu mulki.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Akwai misalan irin wadannan sojojin a wannan yanki na mu ma, wanda wasunsu sama da shekara guda kenan suke amfani da dukkanin karfinsu wajen kai hari wa al'ummar kasar Yemen, duk kuwa da cewa sun gagara aikata komai.

Ayatullah Khamenei yayi ishara da gungu na biyu na sojoji wadanda ya ce su ne: Wadannan sojojin a zahiri suna da karfi na sojoji sosai, to amma a fagen aiki kan babu abin da suka sa a gaba in ban da amfani da karfin sojin, rashin hankali da kuma rashin imani.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana ayyukan sojojin Amurka a kasashen Iraki da Afghanistan a matsayin misalin ayyukan irin wadannan sojojin wadanda ba abin da suka sani in ban da amfani da karfi da nuna rashin imani inda ya ce: Irin wadannan sojojin a duk lokacin da suka fuskanci matsala da gazawa a fagen daga, to kuwa ba su jin kunyan amfani da sojoji marasa hankali da rashin imani wadanda suka kwace wajen aikata laifuka irin su dakarun 'Black Watar'.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Sojoji guda daya tilo a duniyar nan wadanda masu riko da koyarwa ta addini ne sannan kuma ga kwarewar aiki da kuma 'yanci na siyasa wajen aiki a kasarsu, su ne kawai sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Aikin soji a Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba wai wani matsayi ne na jeka na yi ka ba, haka nan kuma ba wani aiki ne maras kwarewa da rashin hankali da rashin manufa ba.

Don haka sai Jagoran yayi kiran da a kara kiyayewa da kuma karfafa irin wannan siffa da sojojin na Iran suke da shi yana mai cewa: Dakarun sojin Iran ba na wani mutum ko wata kungiya ko wata jam'iyya ba ce, face dai na dukkanin al'umma da kasa baki daya ne. A saboda haka wajibi ne aiki kariya da tabbatar da tsaro ya zamanto na dukkanin al'umma.

Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musulunci, sai da babban hafsan hafsoshin dakarun Iran Manjo Janar Firouzabadi ya gabatar da jawabinsa inda yayin da yake gabatar da rahoto kan irin ayyuka da kuma tsare tsaren da sojojin na Iran suke da shi ya bayyana cewar: Dakarun sojin Iran suna ganin kara karfafa kansu da irin kwarewa ta soji da kuma makaman kariya musamman makamai masu linzami masu cin dogon zango da fadada rumbunan irin wadannan makamai a matsayin wani farali da ke kansu, don su sami damar kare mutumci da matsayin addinin Musulunci da kuma tabbatar da tsaron kasar Iran. A saboda haka ne muke ganin gudanar da atisayen soji a irin wannan yanayi da ake ciki a matsayin wani lamari na wajibi, sannan kuma za a ci gaba da yin hakan.

Daga karshe dai Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jagoranci mahalarta taron sallar Azahar da La'asar.

3487366

captcha