IQNA

Amnesty Int. Ta Bukaci Sojoji Su Yi Bayani Kan Kisan Gilla A Zaria Najeriya

23:41 - April 14, 2016
Lambar Labari: 3480321
Bangaren kasa da kasa, Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amnesty International ta bukaci sojojin Najeriya su yi bayani kan kisan gillar mutane 347 suka yi a Zaria a kan mabiya mazhabar shi'a.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai ta tashar Aljazeera cewa, babban daraktan kungiyar a reshenta da ke Najeriya ne ya sanar da hakan, inda ya bayyana cewa bayanan da gwamnatin Kaduna ta bayar kan cewa sojoji sun bizne mabiya mazhabar shi'a 347.

Inda suka saka su a wani makeken kabari guda daya a lokaci guda, ya sanya dole ne sojoji su yi bayani kan wadanda suka aikata wannan ta'asa daga cikinsu domin fuskantar sharia.

Haka nan kuma kungiyar ta ce abin da ya faru yana da matukar sosai rai, kuma tana ci gaba da harhada bayanai kan hakikanin abin da ya faru, wanda za ta fitar nan ba da jimawa ba, dangane kisan da aka yi wa mabiya mazhabar shi’a karkashin jagorancin sheikh Ibrahim Zakzaky.

Ita ma a nata bangaren kotun manyan laifuka ta duniya tana harhada bayanai kan abin da ya faru na kisan gilla kan mabiya mazhabar shi'a a Zaria, bayan da wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama masu zaman kansu suka shigar da kara a kan gwamnatin Najeriya da rundunar sojin kasar kan wannan lamari.

Da zaran an kammala bincike daga bangaren kotun manyan laifuka ta duniya kan lamarin, za ta sanar da mataki na gaba wanda za a dauka kan wannan batu na kisan kisan kiyashi da sojojin najeriya suka yi.

3488598

captcha