Bangaren kasa da kasa, tawagar hubbaren Alawi na gabatar da hidima ga masu ziyar hubbarorin Kazimain a daidai lokacin tunawa da shahadar Imam Musa Kazim (AS).
Kmafanin dillancin labaran iqn aya
nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na hubbaren bAlawi cewa, tawagogi
daga wannan hubbare na bayar da dauki ga masu ziyarar 25 ga watan rajab domin
tunawa da shahadar Imam Kazim (AS) da ke zuwa daga bangarori daban-daban.
Sayyid Isa Kazim daya daga cikin mambobin kwamitin hubbaren Aalawi ya bayyana cewa, bias ga a’ada wannan hubbare mai tsarki yana cikin hidimar masu ziyara a wurare masu tsarki, da hakan ya hada da tarukan tunawa da shahadar Imam Kazim (AS) da ake gudanarwa a irin wannan lokaci.
Miqdad Khurasani daya daga cikingudanar da wadannan ayyuka na hidima daga hubbaren alawi mai tsarki, ya bayyana cewa kimanin utane 80 ne suke gudanar da wannan aiki, da suka fito daga tawagar Qamar bani Hashem daga Basara, sai kuma tawagar Amirul muminin (AS) daga Hillah.
Miqdad Khurasani ya kara da cewa, hubbaren Alawi mai alfarma na bayar da abinci dauri dubu 15 a kowace raa ga masu ziyarar Imam Musa Kazim (AS) kamar yadda kumayake bayar da ruwa na sanyi ko na zafi gare su tsawon sa’oi 24 kowace rana.