IQNA

Gasar Kur’ani A Iran Ta Kayatar Da Ni Matuka

23:55 - May 18, 2016
Lambar Labari: 3480425
Bangaren kasa da kasa, wanda ya wakilci kasar Kenya a gasar kur’ani ta duniya daga kasar Kenya ya bayyana gamsuwarsa matuka dangane da yadda gasar ta gudana.

Abdullah Yusuf Isma’ila mahardacin kur’ani mai tsarki daga kasar a zantawarsa da kamfanin dillancin labaran Kur’ani na Iqna ya bayyana cewa, hakika ya karu da abubuwa da dama a halartar gasar kur’ani da ya yi a Iran.

Dangane da yadda alkalai suka gudanar da alkalacin gasar kuwa ya bayyana cewa, a gani na alkalai sun yi iyakacin kokarinsu domin tabbatar da cewa sun yi adalci yadda ya kamata a wannan gasa.

A bangaren matsayin gasar gasar kuwa ya bayyana cewa, duk da cewa dan kasar Masar neya zo na biyu a wannan gasa abangaren harda, wannan shi ma abin farin ciki ne gare shi domin kuwa daga nahiyarsa yake.

Ya ce wannan shine karon farko da ya zo kasar Iran, kumaya zo domin gasar kur’ani, amma a hakikanin gaskiya ya karu da abubwa da dama da suka kara masa ilimi da sanin yanayin al’ummomi, musamman ma al’ummar wannan kasa.

Abdullah Yusuf y ace kasar Masar it ace kasar farko da ya fara zuwa domin gasar kur’ani, kuma ya samu matsayi a cikin wadanda suke gaba-gaba, kamar yadda a gasar Iran ma yaje har zuwa zagaye na biyu, wanda hakan babban abin alfahari ne a gare shi.

Daga karshe ya bayyana fatansa dangane da wannan gasa, na ganin cewa an ci gaba da gudanar da ita kamar yadda ake tsawon shekaru talatin da uku da suka gabata, tare da kara samun ci gaba da kuma kara wayar da kan musulmi damgane da kur’ani da kuma wajabcin aiki da shi a tsakanin al’ummar musulmi, wanda shi ne mafita kuma abin da zai hada kanmu baki daya.

3498987

captcha