IQNA

Babban Kwamandan Askarawa:

Ma’abota Girman Kai Sun Fusata Kan Babban Jihadin Al’ummar Iran

23:52 - May 24, 2016
Lambar Labari: 3480443
Bangaren siyasa, a lokacin da jagoran juyin Islama yak e gabatar da jawabi a gaban daliban jami’ar soji ta Imam Hussain (AS) ya bayyana cewa; rashin bin salon siyasa da tatalin arziki turawa shi ne babban jihadi.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jagora cewa, a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan zagayowar ranar 3 ga watan Khordad, ranar da aka kwato garin Khoramshahr daga hannun sojojin kasar Iraki, a safiyar yau Litinin (23-05-2016) ne Jagoran juyin juya halin Musulunci kuma babban kwamandan dakarun kasar Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya halarci bikin yaye daliban jami'ar Imam Husaini (a.s) ta soji ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci.

Tun da farkon isowarsa wajen bikin, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya fara ne da ziyartar makabartar shahidan Jami'ar inda ya karanta musu Fatiha da roka musu karin matsayi a wajen Allah Madaukakin Sarki. Daga nan kuma sai ya wuce zuwa wajen sojojin da suke tsaye cikin layin don duba su da isar da gaisuwa a gare su. Kamar yadda kuma ya tafi wajen sojojin da suka sami raunuka a wajen yaki ciki kuwa har da dakarun sa kai da suka tafi Siriya da nufin kare hubbarorin Ahlulbaiti (a.s) daga hare-haren 'yan ta'adda da kuma wasu daga cikin iyalan shahidan don isar da gaisuwarsa da kuma jinjina musu.

A jawabin da ya gabatar a wajen bikin, Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayi karin haske dangane da hikimar Alkur'ani mai girma da kuma addinin Musulunci dangane da batun 'Jihadi Mai Girma' wato "tsayin daka da kuma kin mika wuya ga ma'abota girman kai" bugu da kari kan bangarorisa cikin tsarin Jamhuriyar Musulunci. Har ila yau kuma yayin da yake ishara da kokari da tsare-tsaren da ma'abota girman kai suke yi wajen yin tasiri da kuma sauya yanayin tsarin Musulunci na Iran, Jagoran ya bayyana cewar: Mafi muhimmancin nauyin da ahalin yanzu yake wuyan cibiyoyi ilimi na jami'oi da makarantun addini, bugu da kari kan matasa muminai masu riko da juyin juya halin Musulunci, haka nan kuma da cibiyar dakarun kare juyin juya halin Musuluncin shi ne "aiki cikin hikima da hangen nesa wajen bayani da wayar da kan al'umma dangane da ma'anonin taken juyin juya halin Musulunci da kuma nesantar aiwatar da wasu abubuwa marasa amfani, yin ayyuka saboda makomar kasa da kuma tattarowa da kuma tsara irin kwarewa mai ban mamaki da aka samu tsawon shekaru 37 da nasarar wannan juyin juya hali.

Haka nan kuma yayin da yake taya al'umma murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Mahdi (Allah Ya gaggauta bayyanarsa) haka nan kuma da ranar 3 ga watan Khordad, wato ranar da aka 'yanto garin Khoramshahr daga hannun sojojin mamayan kasar Iraki yayin kallafaffen yaki, Jagoran ya bayyana wannan ranar a matsayin daga cikin ranakun da ba za a taba mantawa da su ba cikin tarihin juyin juya halin Musulunci kana kuma wata alama ce ta karfin Ubangiji inda ya ce: Dangane da hare-haren soji da aka tsara su da nufin 'yanto garin Khoramshahr da ma sauran hare-haren da aka kai yayin kallafaffen yaki, akwai wasu bayanai masu yawan gaske da watakila da dama daga cikin mutanen kasar nan musamman matasa ba su da labarinsu. A saboda haka ne na ke kira zuwa ga karanta littafan da suke da alaka da kallafaffen yakin.

Haka nan yayin da yake ishara da daya daga cikin batutuwa masu muhimmanci dangane da harin 'yanto garin Khoramshahr, Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayi ishara da irin karfi da kuma taimakon Ubangiji da ke cikin hakan inda ya ce: Marigayi Imam Khumaini, wannan babban bawan sannan mutum ma'abocin hikima na hakika ya bayyana cewar Allah ne ya 'yanto garin Khoramshahr.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: A bisa wannan mahangar, a yayin da aka yi dukkanin kokari da aikin da ya kamata a yi, aka shigo da dukkanin karfin da ake da shi cikin fage sannan kuma daga karshe aka mika komai ga Allah, to kuwa a nan ne taimakon Allah zai shigo fage. Sakamakon hakan kuwa shi ne 'yantar da garin Khoramshahr daga hannun makiya wadanda suke da dukkanin makaman da ake bukata.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Da irin wannan mahangar, to lalle akwai yiyuwar 'yanto dukkanin duniya daga hannun ma'abota girman kai, haka nan kuma da kasar Palastinu da kuma samar da yanayin da zai zamanto babu wata al'umma mai rauni da za ta saura a duniyar nan.

Jagoran ya jaddada cewar: Duk wata al'ummar da take da irin wannan mahangar sannan kuma ta yi amfani da dukkanin karfi da kwarewar da take da su kana kuma ta dogara da Allah, to ko shakka babu za ta zamanto ta razana da karfin soji, dukiya, kafafen watsa labarai da kuma siyasa da ma'abota girman kai suke da su ba.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da kokarin da ma'abota girman kai suka dinga yi tsawon shekaru 38 din da suka gabata wajen durkusar da juyin juya halin Musulunci na Iran amma sun gagara ba, duk kuwa da amfani da duk wani karfin da suke da shi da makirce-makircen da suka kulla, Jagoran ya bayyana hakan a matsayin wani misali na fili na nasarar mahangar kokari da tsayin daka da kuma dogaro da Allah Madaukakin Sarki. Daga nan sai ya ce: Al'ummar Iran dai tana nan a fage, sannan kuma akwai matasa da yawan gaske da suke shirye su sadaukar da rayukansu saboda wannan juyin juya halin Musuluncin. To wannan shi ne abin da yake janyo taimakon Allah.

Ayatullah Khamenei ya bayyana irin wannan fito na fito da ma'abota girman kai a matsayin 'wani yaki da ba za a iya kwatanta karfin juna ba' daga nan sai ya ce: A yayin wannan yakin, dukkanin bangarori biyu suna da karfi da karewar da daya bangaren ba ya da su. Tushen karfi gwamnatin Musulunci, shi ne dogaro da karfi da kudurar Ubangiji da kuma dogaro da karfi da iradar mutane muminai.

Haka nan kuma yayin da yake bayyana cewar irin wannan yakin wani yaki ne na irada da karfi, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: A fagen wannan yakin, a duk lokacin da irada da karfin daya bangaren yayi rauni da jijjiga, to ko shakka babu zai sha kashi. A saboda haka wajibi ne mu yi taka tsantsan wajen ganin farfaganda da kuma sanya waswasin makiya ba su haifar da gibi cikin iradar mu ba.

Jagoran ya bayyana wannan yakin a matsayin yakin da ya dara yaki na soji kana kuma wani nau'ii na jihadi inda ya ce: A halin yanzu dai yiyuwar kaddamar da yaki na soji a kan kasar mu yana da rauni sosai, to amma batun jihadi yana nan. Wannan jihadin wanda yayi daidai da hikima da koyarwa ta Alkur'ani da Musuluni shi ne jihadi mai girma, wato tsayin daka, gwagwarmaya da kin bin kafirai da mushirikai.

Haka nan kuma yayin da yake bayyana cewar wannan jihadi mai girma yana nan hatta a fagagen siyasa, tattalin arziki da al'adu, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: A dukkanin wadannnan fagagen, maimakon biyayya ga sansanonin kafirai da mushirikai, wajibi ne a yi biyayya da kuma koyi da tsare-tsare da ayyuka na Musulunci da Alkur'ani.

Jagoran ya bayyana cewar matsalar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ma'abota girman kai a halin yanzu matsala ce ta "biyayya" don haka sai ya ce: Wadannan mutanen sun yi amfani da dukkanin kayan aikinsu, matsin lamba da makirce-makirce na al'adu, tattalin arziki, siyasa da farfaganda bugu da kari kan amfani da 'yan amshin shatansu don su dunkufar da gwamnatin Musulunci da kuma tilasta mata yi musu biyayya. To amma abin da ya ke sanya ma'abota girman kan fushi da kiyayya da al'ummar Iran, shi ne cewa al'ummar (Iran) saboda kasantuwarsu musulmi ba a shirye su ke su mika kai da yin biyayya ga ma'abota girman kai ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa gabatar da batutuwa irin su batun nukiliya, karfin makamai masu linzami da take hakkokin bil'adama wata hanya ce da ma'abota girman kan suke fakewa da su don cimma manufofinsu inda ya ce: babban dalilin dukkanin wannan kiyayyar da fakewa da wasu abubuwa, shi ne kin mika kai ga ma'abota girman kai. Don kuwa da a ce al'ummar Iran a shirye take ta mika kai, ko shakka babu da sun rufe ido kan batun makamai masu linzami da nukiliya. Haka nan kuma ba za ka taba jin sun kawo maganar take hakkokin bil'adama ba.

Dangane da batun makamai masu linzami na Iran, Ayatullah Khamenei yayi ishara da wani batu inda ya ce: A baya-bayan nan sun tada jijiyoyin wuya kan batun karfin makamai masu linzami da mukeda shi. To amma ya kamata su san cewa irin wadannan ihu bayan hari ba za su yi mana wani tasiri ba, sannan kuma babu wani abin da za su iya.

A ci gaba da karin bayani dangane da dalilan da ya sanya makiya ci gaba da kiyayya da tsarin Musulunci na Iran, Jagoran ya bayyana cewar: Amurkawa suna ta kokari wajen ganin ba su fitar da wannan gabar a harshensu ba, to amma a wasu lokuta maganganunsu sukan fasa musu kwai. Kamar yadda cikin 'yan kwanakin da suka gabata wani jami'in Amurka bayan sake jaddada irin tuhumce-tuhumcen da suka saba yi wa Iran, ba tare da son sa ba ya kawo batun akida wato wannan koyarwa ta Musulunci wanda ita ce ta hana al'ummar Iran mika kai ga sansanin kafirai da ma'abota girman kai.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana "tsayin daka", "rashin biyayya ga makiya" da kuma "kiyaye koyarwar juyin juya hali da kuma Musulunci" a matsayin tushen karfi da tsayin daka gwamnatin Musulunci da al'ummar Iran. Daga nan sai ya ce: Amurka da sauran ma'abota tinkaho da karfi na duniya suna tsananin bakin ciki da wannan batun, sannan kuma ba su da abin da za su iya. A saboda haka ne suke ta kokari ko za su sami damar janyo manyan jami'an kasar nan zuwa gare su. Amma sun gaza, kuma da yardar Allah ba za su iya ba.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Babban aikin dakarun kare juyin juya halin Musulunci shi ne "ba da kariya ga juyin juya hali". A saboda haka wajibi ne babban jihadi ya zamanto shi ne tushen tsare-tsaren dakarun kare juyin juya halin Musuluncin.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin gagarumar farfaganda da tuhumce tuhumce da ake yi wa dakarun kare juyin, Jagoran ya bayyana cewar: Babban dalilin wannan fushin, shi ne tsayin dakan dakarun kare juyin a bisa tafarkin juyin juya hali da kiyaye mahangar da aka dauka da kuma ruhin Musulunci da kuma juyin juya hali.

Daga nan sai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kirayi matasan Iran da daliban jami'ar sojin da suke wajen da cewa: Makomar juyin nan tana hannunku, ku din nan ne ya zama wajibi ku kiyaye wannan tarihi cikin izza da daukaka. Ku san cewa a nan gaba akwai Khoramshahr da yawa; ko da yake ba wai a fagen yaki na soji ba, face dai a fagagen da ba su da irin yanayin ruguza gari da yaki yake haifarwa, face dai a fagen sake gina kasa, duk kuwa da cewa ya fi yaki na soji wahala da tsanani.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da karin bayani dangane da bangarori daban-daban na 'Jihadi mai girma' a fagagen tattalin arziki, al'adu da kuma zamantakewa inda ya ce: Jaddadawar da nake yi dangane da batun aiwatar da siyasar tattalin arziki ta dogaro da kai, wani bangare na wannan jihadi a fagen tattalin arziki.

Haka nan yayin da yake ishara da tuhumce-tuhumce marasa tushe da wasu 'yan adawa suke yi ga wannan yunkuri da ikirarin cewa dogaro da irin karfi na cikin gida da ake da shi yana nufin katse alaka da kasashen duniya ne, Jagoran ya bayyana cewar: Mu dai babu wani lokaci da muke maganar katse alaka da duniya da kuma killace kammu mu kadai. Face dai muna fadin cewa ne ana iya kulla alaka ta siyasa da kasuwanci da kasashen duniya, to sai dai a kiyaye mutumci da daukakar da ake da ita. A lokacin da muke son magana ko kuma mu kulla wata yarjejeniya, to mu dinga magana a matsayin wakilan kasar Musulunci ta Iran da kuma wakilan Musulunci, sannan mu zauna a kan teburin kulla yarjejeniya cikin hayacinmu da kuma sanin ya kamata.

Haka nan kuma yayin da yake jaddada cewar Jihadi mai girma yana bukatar taka tsantsan da kuma ikhlasi da tsarkin zuciya, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da kokari da fatan da makiya suke da shi na samun kutsawa da kuma tasiri cikin Iran inda ya ce: A halin yanzu dai makiya sun yanke kaunar cutar da tsarin Musulunci gagarumar cutarwa, to amma ta hanyar amfani da hanyoyi daban-daban kana kuma masu sarkakiya suna neman samun tasiri a cikin Iran don juya yanayi da tunanin matasan Iran zuwa ga irin yadda Amurka take so. Don kuwa ta hakan ne za su sami cimma manufofinsu ba tare da wata wahala ba.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar kuskuren fahimtar al'ummar Iran da Amurka da sauran ma'abota girman kai suka yi ne ya sanya suke daukar matsaya da suke cike da kura-kurai. Don haka sai ya ce: Koda yake tabbas ba su yanke kaunar samun tasiri din. Don haka a irin wannan yanayin akwai wani gagarumin nauyi a wuyan dukkanin al'ummar Iran da kuma wadanda suke da alaka da tsarin Musulunci ciki kuwa har da dakarun kare juyin juya halin Musulunci.

Haka nan yayin da yake jaddada cewar wajibi ne dakarun kare juyin juya halin Musulunci a koda yaushe su zamanto cikin shirin ko ta kwana na soji, Jagoran ya ce: Koda yake nauyin da ke wuyan dakarun kare juyin ba wai kawai ya tsaya a fagen daga na soji ba ne, face dai a wannan lokacin daya daga cikin nauyin da ke wuyan dukkanin masu kishi da kuma kaunar juyin juya halin Musulunci cikin kuwa har da dakarun kare juyin shi ne bayani da wayar da kan al'umma dangane da hakikanin juyin nan da kuma koyarwarsa.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kirayi kowa da kowa zuwa ga ba da muhimmanci ga batun wayar da kan al'umma yana mai cewa: Bayanin taken juyin juya halin Musulunci da kuma hakikani da ma'anoninsu, lamari ne da zai bayyanar da ingantaccen tafarkin juyin da kuma tafarkin gaskiya.

Haka nan yayin da yake magana dangane da irin juya bayan da wasu suka yi a lokuta daban-daban na wannan juyin, Jagoran ya bayyana rashin fahimtarsu ga hakikanin yanayi a matsayin ummul aba'isin din hakan yana mai cewa: Wajibi ne a yi tunani sosai dangane da asalin take da koyarwar juyin juya hali sannan kuma a nemi shawarwari da shiryarwar salihan malamai.

A karshen jawabin nasa, Ayatullah Khamenei yayi karin haske dangane da wajibin karfafa alaka da Allah Madaukakin Sarki, riko da karatun Alkur'ani da tunani cikin ayoyinsa, tsai da salla da kuma amfani da damar da ke cikin watannin Sha'aban da Ramadhan.

A yayin bikin, babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musuluncin Manjo Janar Muhammad Ali Ja'afari ya gabatar da jawabinsa inda ya ce babban dalilin irin karfin da tsarin Musulunci na Iran yake da shi shi ne tsayin dakansa a gaban wuce gona da irin Amurka. Daga nan sai ya ce: Dakarun kare juyin sun ba da dukkanin himmarsu wajen ruguza makirce makircen makiya ta hanyar karfafa irin karfin da suke da shi na karen juyi, dubi cikin tafarkin juyin da kuma aiwatar da tunani da koyarwar Jagoran juyin juya halin Musulunci a aikace.

Yayin da yake ishara da makirce-makirce da neman tsokanar da wasu kasashen da aka bar su a baya suke don cimma manufofin Amurka a kan Iran, Manjo Janar Ja'afari ya bayyana cewar: Farkawa da gwagwarmayar Musulunci suna nan daram sannan kuma makirce-makircen 'yan mulkin mallaka ba za su hana ci gaban juyin juya halin Musulunci da kuma farkawa ta Musulunci.

Janar Ja'afari ya ci gaba da cewa: Matasa dakarun kare juyin suna cikin shiri fadawa fagage masu wahala da sarkakiya don kare daukakar Musulunci da kuma tsarin Musulunci.

Har ila yau kwamandan jami'ar ta Imam Husain (a.s) Admiral Murtadha Safari shi ma ya gabatar da jawabinsa inda yayi karin haske dangane da ayyukan da ake gudanar a jami'ar.

Daga karshe dai daliban jami'ar sun gudanar da fareti da kuma wasu atisaye na soji don nuna irin kwarewar da suke da ita.

3500433

captcha