Yayin da yake ishara da mganganun mai girma Amirul Muminin (a.s) dangane da abin da ya kamata a aikata yayin da ake fuskantar matsala ta fitina a tsakanin al'umma, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Imam Ali (a.s) ya kasance yana kiran mutane zuwa ga aikata abubuwan da ba za su taimaka wajen ci gaba da ruruta wutar fitina ba a yayin da suka sami kansu cikin yanayi na fitina da bambance gaskiya da karya ya zamanto da wahala.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: A yayin da fitina ta kunno kai, misali irin fitinar da ta faru a shekara ta shekarar 1388 (2009 bayan zaben shugaban kasa a kasar Iran), bai kamata magana, shiru ko kuma aikin da za mu yi, su zamanto masu taimaka wa karfafa fitinar ba.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Mai yiyuwa wasu mutane saboda ra'ayi da kuma mahangar da suke da ita ya zamanto ba sa son fitowa fili wajen fada da fitinar, to amma bai kamata su bari a yi amfani da su wajen karfafa fitinar ba.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da wata maganar hikima ta Amirul Muminin (a.s) a cikin littafin Nahjul Balagan, Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayi ishara da batun kwadayin shugabanci don cimma wata manufa ta tara dukiya ko kuma wata dama ta daban, inda yace: A gaskiya irin wannan kallo ga shugabanci wanda a hakikanin gaskiya wata amana ce, lamari ne da zai kaskantar da mutum da mai she shi ba a bakin komai ba.
A saboda hakan ne ma Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da batun albashi mai yawan gaske da ake zargin wasu jami'an gwamnati da dauka inda ya ce: Batun irin wannan gagarumin albashi wani lamari da bai dace ba, to amma ya kamata kowa ya san cewa wannan lamarin nadiran ake samun faruwar hakan, don kuwa mafiya yawan jami'ai da manyan daraktocin gwamnati mutane ne tsarkaka. To amma dai samun 'yan wannan tsiraru din ma wani abu ne mai muni, wanda wajibi ne a yi fada da hakan.
Haka nan kuma yayin da yake magana kan umurnin da shugaban kasa da mataimakinsa suka bayar da gudanar da bincike kan wannan lamarin don daukan matakan da suka dace, Jagoran ya bayyana cewar: Bai kamata a yi sako sako da wannan batu ba, wajibi ne a ba shi dukkanin muhimmanci. Sannan kuma a sanar da mutane sakamakon binciken.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: Bisa bayanan da suka shigo hannuna, abubuwan da manyan jami'ai da daraktoci suke dauka a matsayin albashi wani abu ne da yayi daidai da hankali, wasu 'yan tsirarrun jami'ai da daraktocin ne suke diban irin wadannan kudade na hauka, wanda wajibi ne a yi fada da hakan ma.
A karshen jawabin nasa, Ayatullah Khamenei yayi ishara da wata hikimar ta Amirul Muminin (a.s) a cikin littafin Nahjul Balagan inda ya ce: Wajibi ne a koda yaushe mu yi taka tsantsan da harsunanmu, don kuwa mafiya yawa daga cikin matsalolin dan'adam sun samo asali ne daga harshensa.
Jagoran ya ci gaba da cewa: A wasu lokuta matsalolin da suke kunno kai sakamakon rashin kula da kuma kiyaye harshe suna da bangare na daidaiku, to amma a wasu lokuta matsalolin suna shafan al'umma. Don haka wajibi ne a lura sosai.
Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musulunci, sai da shugaban kasar Iran Hujjatul Islam wal muslimin Hasan Ruhani ya gabatar da jawabinsa da kuma karin bayani kan wasu daga cikin ayyuka mafi muhimmanci da gwamnatin tasa ta aikata.
Daga karshe dai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jagoranci mahalarta taron sallolin Magariba da Lisha kana daga baya kuma suka sha ruwa tare.